Sinawa da suke dukufa wajen kare kwararowar hamada
2021-08-25 17:40:44 CRI
"Kakana da mahaifina dukkansu masu aikin kula da dazuzzuka ne, a nan aka haife ni, a nan kuma na girma. Zan yi kokarin kare dazuzzukan, don kiyaye nasarorin da tsoffinmu suka samu, kuma mu ci gaba da wannan aikin da suka gudanar har zuwa zuriyoyinmu na gaba."
Malam Jia Wenyi yana da shekaru 53 da haihuwa, kuma yau shekaru 36 ke nan yana gudanar da aikin kula da dazuzzuka da kare kwararowar hamada a hamadar Kubuqi da ke arewacin kasar Sin, Kamar dai yadda kakansa da mahaifinsa suka yi, malam Jia Wenyi ma ya sadaukar da rayuwarsa ga aikin yaki da kwararowar hamada da kare dazuzzuka. To amma me ya sa malam Jia Wenyi da mahaifinsa da ma kakansa, wato zuriya uku na wannan iyali, su ka shafe kimanin shekaru 70 suna gudanar da aiki guda a cikin wannan hamadar? Cikin shirinmu na yau, za mu ji daga bakin su.(Lubabatu)