logo

HAUSA

Duniya ba za ta yarda da karairayin da hukumar leken asirin Amurka take kitsawa ba

2021-08-25 21:40:08 CRI

Duniya ba za ta yarda da karairayin da hukumar leken asirin Amurka take kitsawa ba_fororder_A

Jiya Talata 24 ga wata, wa’adin kwanaki 90 na binciken asalin kwayar cutar COVID-19 da gwamnatin Amurka ta baiwa hukumar leken asirin kasar ya cika, inda mai magana da yawun fadar White House ta ce, nan da wasu kwanaki za’a fitar da rahoto kan sakamakon binciken ga duk duniya. Duk wani sakamakon binciken da rahoton zai gabatar, baiwa hukumar leken asiri wannan aiki, dambarwar siyasa ce kawai.

“Muna karya, muna yaudara, muna sata ……” abun da tsohon sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya ce ya shaida abubuwa na rashin kirki da hukumar leken asirin kasar ta kan yi. Kana tarihi ya nuna cewa, Amurka ta kan yi amfani da hukumar leken asirin ta, don nuna babakere a duniya, kuma muggan abubuwan da ta yi ba sa misaltuwa.

Duniya ba za ta yarda da karairayin da hukumar leken asirin Amurka take kitsawa ba_fororder_B

Bai kamata a siyasantar da harkokin kimiyya ba. Game da asalin kwayar cutar COVID-19, rahoton bincike na hadin-gwiwar Sin da hukumar WHO da aka fitar a karshen watan Maris din bana, ya riga ya sanar da sakamakon da kasa da kasa gami da masana kimiyya suka amince da shi, wato babu yiwuwa kwayar cutar ta bulla daga cikin dakin gwajin dake kasar Sin.

Har kullum kasar Sin tana goyon-baya kana za ta ci gaba da shiga ayyukan binciken asalin cutar, amma ko ta yaya ba za ta yarda da abun da hukumar leken asirin Amurka ta yi ba, na shafa mata bakin fenti. Kana duk duniya ma ba za ta yarda da irin wannan rahoton dake cike da karairayi ba wanda aka shafe tsawon kwanaki 90 ana yi kuma ta hanyar da ba ta dace ba. Kusan kasashe 80 sun gabatar da wasika ga babban darektan hukumar WHO ko kuma fitar da sanarwa ko kiran taro don nuna adawar su ta siyasantar da batun binciken asalin cutar COVID-19, wannan babbar shaida ce. (Murtala Zhang)