logo

HAUSA

Masar ta karrama ‘yan wasan ta da suka lashe lambobin yabo a gasar Olympic ta Tokyo

2021-08-25 16:34:36 CRI

Masar ta karrama ‘yan wasan ta da suka lashe lambobin yabo a gasar Olympic ta Tokyo_fororder_masar-1

Masar ta karrama ‘yan wasan ta da suka lashe lambobin yabo a gasar Olympic ta Tokyo_fororder_masar-2

‘Yan wasan motsa jiki na kasar Masar su biyu, karateka Feryal Ashraf Abdelaziz, da Ahmed Elgendy, sun samu gagarumar tarba yayin da suka sauka a filin jirgin saman birnin Alkahira, bayan kammala gasar Olympians ta birnin Tokyo, tare da lashe lambobin yabo. Dandazon al’ummar Masar masu kaunar wasanni ne suka tari ‘yan wasan a filin jirgin saman cike da murna da jinjina gare su.

karateka Feryal Ashraf Abdelaziz dai ta lashe lambar zinari ne a gasar Kareti nau’in “Kumite” ajin mata masu nau’in sama da kilogoram 61, yayin da Ahmed Elgendy, ya lashe lambar azurfa a gasar “modern pentathlon” ajin maza, wato gasar hadakar wasanni 5 da suka hada da harbin bindiga, da iyo, da fadan takobi, da tsere, da tsallake shinge kan dawaki.

Bisa jimilla, Masar ta lashe lambobin yabo 6, da suka hada da zinari 1, azurfa 1, da tagulla 4 a gasar ta birnin Tokyo da aka rufe a karshen makon jiya, kuma a wannan karo ne Masar din ta fi lashe lambobin yabo a dukkanin gasannin Olympic da ta taba halarta.

Feryal Ashraf Abdelaziz, ta zamo mace ta farko da ta ciwa Masar lambar zinari a tarihin zuwan kasar gasar Olympic, kuma lambar zinari ta farko da Masar din ta samu a wannan gasa, tun bayan wadda kasar ta lashe a gasar birnin Athens a shekarar 2004, kuma a karo na 8 na halartar gasar Olympic da kasar ke halarta tun daga shekarar 1912.

Da yake tsokaci game da nasarar da ta cimma, daya daga ‘yan uwan ‘yar wasan Ahmed Samy, ya ce "Ina alfahari da ita. Daukacin al’ummar Masar na matukar alfahari da nasarar da ta cimma.

Amned mai shekaru 30, wanda ya zanta da kamfanin dillancin labarai na Xinhua lokacin da yake dakon saukar ‘yar wasan daga jirgin sama, ya ce abokai da masu sha’awar wasanni sun taru a filin jirgin domin maraba da dawowar ta, tare da fatan jinjina mata. Ya ce "Ta yi aiki tukuru cikin shekarun da suka gabata, domin kaiwa ga cimma nasara. Ko shakka ba bu ta cancanci samun nasara".

Yayin da ‘yan wasan 2 suka sauka, sai suka shiga wata mota kirar bas suna rike da lambobin yabon da suka lashe, tare da dagawa masoyan su hannu, yayin da masu goya musu baya ke Shewa da jinjina musu.

Shi ma Amr Khaled, aboki ga Elgendy, ya ce ya zo filin jirgin saman ne domin karrama ‘yan wasan. Ya kuma shaidawa Xinhua cewa, “Elgendy ya samu horo mai nagarta cikin watanni kadan kafin halartar gasar, kuma ya tafi da niyyar samowa Masar lambar yabo. Ya ce “Ina matukar alfahari da nasarar da ya samu".

Kaza lika a cewar matashin, har kullum Elgendy na fatan cimma nasarori, kuma a baya ya taba lashe lambobin yabo a gasannin kasa da kasa da ya halarta, da na yankuna, da ma wadanda ake yi a cikin gida.

A wani ci gaban kuma, ministan ma’aikatar wasanni da matasa Ashraf Sobhy, ya shaidawa ‘yan jarida a filin jirgin cewa, ‘yan wasan Masar sun samarwa kasar martaba, ta hanyar lashe lambobin yabo. Ya ce gwamnatin kasar na shirin samar da wani sabon rukuni na ‘yan wasan Olympics, kuma shugaban kasar Abdel-Fattah al-Sisi, na samar da dukkanin goyon baya kan hakan, ga dukkanin ‘yan wasan dake wakiltar kasar a gasar Olympics, da ma kwamitin shirya gasar na kasa.

Tun daga shekarar 1912 da Masar ta fara halartar gasar Olympics a karo 23, ta lashe jimillar lambobin yabo 38, da suka hada da na zinari 8, da azurfa 11, da tagulla 19.