logo

HAUSA

Mai Hakuri Ya kan Dafa Dutse

2021-08-25 16:29:02 cri

Fiye da mutane dubu ashirin ne, suka halarci kasaitaccen bikin da aka shirya a birnin Lhasa, fadar mulkin jihar Tibet na kasar Sin, domin murnar cikar yankin shekaru 70 da samun ’yanci cikin ruwan sanyi. Bikin da ya gudana ranar Talata 19 ga watan Agustan shekarar 2021.

Tarihi ya nuna yadda a baya wannan yanki, ya yi fama da matsalar rashin muhimman ababan more rayuwa, kamar hanyoyin mota, da layin dogo da filayen jiragen sama, da sauransu. Sai dai bisa namijin kokarin bangarori daban-dabab na kasar Sin, kwanci tashi yankin ya bunkasa, har ya kai ga samun gagarumin ci gaban tattalin arziki, da ba a taba ganin irinsa ba a tarihi. Mahakurci, mawada ci ne.

Gwamnatin tsakiyar kasar Sin ta mayar da hankali wajen raya tattalin arzikin Tibet da ma kyautata zaman rayuwar al’ummar yankin. Matakin da yanzu haka, ya kara janyo masu sha’awar gudanar da harkokin kasuwanci zuwa yankin. 

Rahotanni na nuna cewa, kafin ’yantar da yankin Tibet cikin lumana, adadin wadanda ba sa iya karatu da rubutu a yankin, ya wuce kaso 95 cikin dari. Amma a halin yanzu yankin Tibet ya zama na farko a kasar Sin, wadda ke ba da ilmi kyauta na tsawon shekaru 15. Haka kuma, yankin ya kafa cikakkun tsare-tsaren kiwon lafiya, da kulawa da mata da kananan yara, dakile da kandagarkin cututtuka, da ilmin likitanci na kabilar Tibet da ilmin magungunan gargajiya na kabilar Tibet. Yanzu haka, matsakaicin tsawon ran mazauna Tibet ya zarce shekaru 71 a shekarar 2019, a maimakon 35.5 shekaru 70 da suka gabata.

Wani muhimmin batu shi ne, tun bayan babban taron wakilan JKS karo na 18 a shekarar 2012 zuwa yanzu, yankin Tibet ya kasance cikin wani sabon zamani, inda ya fi samun ci gaba da babban sauyi, mazauna yankin sun fi samun alheri. Ban da haka kuma, matsakaicin saurin ci gaban tattalin arzikin yankin na Tibet a kowace shekara, yana matsayi na uku na farko a kasar Sin. Saurin karuwar matsakaicin kudin shigar kowane mazauni Tibet dake yankin karkara, yana matsayi na farko a kasar Sin a shekaru da dama a jere. Wani abin farin ciki ma shi ne, yankin Tibet da sauran sassan kasar Sin, sun yi nasarar kafa al’umma mai matsakaiciyar wadata ta kowacce fuska daidai lokacin da aka tsara.

Sanin kowa ne cewa, yanzu kasar Sin tana cikin wani muhimmin lokaci na cimma burin farfado da al’ummar Sinawa. Ta kuma yi nasarar kaddamar da sabon aikin raya kasa na gurguzu na zamani daga dukkan fannoni. Yankin Tibet shi ma yana matsayi na sabon mafari na bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al’umma.

Sakamakon wadannan ci gaba da yankin ya samu, ya sa mazauna yankin suka lashi takwabin yakar duk mai neman kawo wa yankin da ma kasar Sin baki daya baraka, kuma abokan gabansu, ba za su cimma burinsu ba.” Yanzu haka , mazauna yankin Tibet sun fita daga tarin matsalolin da suka fuskanta a baya, abin da ke nuna cewa, duk wani yanki da ya yi hakuri, ya kuma dauki matakan da suka dace wajen samarwa kansa mafita, komai dadewa, hakarsa za ta cimma ruwa. Ci gaban yankin na Tibet, wata babbar nasara ce, ga manufofin kasar Sin na raya yankunan kananan kabilun kasar. (Ibrahim Yaya)