logo

HAUSA

Ya kamata dangantakar Sin da Kasashen Larabawa ta kasance darasi ga duniya

2021-08-24 20:27:12 cri

Ya kamata dangantakar Sin da Kasashen Larabawa ta kasance darasi ga duniya_fororder_微信图片_20210824202544

An kammala taron baje koli na hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Larabawa, da ya aka yi a Yinchuan, babban birnin jihar Ningxia ta Hui mai cin gashin kanta dake arewa maso yammacin kasar Sin, wanda ya shaida ya rattaba hannu kan yarjeniyoyi cinikayya 277 da darajarsu ta kai yuan biliyan 156, kwatankwacin dala biliyan 24.

Dangantakar Kasashen Sin da na Larabawa ta jima da kulluwa tun lokacin cinikin siliki, inda ya yi ta habaka da samun armashi har zuwa wannan lokaci da muke ciki. Duk kuwa da annobar COVID-19 da ake fuskanta, dangantakar ta su na nan da karfinta. Kasar Sin ta kasance babbar abokiyar cinikayyar kasashen Larabawa, inda a bara, darajar cinikayya a tsakaninsu ta kusa kai wa dala biliyan 240.

Baje kolin na yini 5 da aka kammala a farkon makon nan, hakika zai haifar da sabon zarafi da kara zaburar da kasashen yayin da duniya ke fuskantar matsalar annobar COVID-19 da ta kawo koma bayan tattalin arziki. Haka zalika, ya nuna irin hangen nesan kasar Sin da ma kasashen na Larabawa, wato yayin da ake yaki da annoba da sauran wasu matsalolin da ake fuskanta a duniya, ba su yi kasa a gwiwa ba wajen raya hadin gwiwarsu da neman hanyoyin ci gaba da wadata.

Yarjeniyoyin 277 da aka kulla tsakanin bangarorin yayin baje kolin, sun shafi fannonin da suka hada da tattalin arzikin zamani da makamashi mai tsafta da albarkatun ruwa da aikin gona na zamani da cinikayya ta intanet da kayayyakin abinci da kuma yawon bude ido. Wannan ya nuna kudurin kasashen na fadadawa da zurfafa dangantakarsu, ta yadda za ta tafi da zamani da kawo dimbin alfanu ga jama’arsu. Kana matsayinsu na masu rajin tabbatar da tsarin huldar kasa da kasa baje kolin ya nuna manufar ta su a aikace, wato ba abu ne da ya tsaya a fatar baki ba. Ya kamata wannan ya zamarwa duniya darasi kuma misali, ganin irin dimbin alfanun da aka samu daga hadin gwiwar da aka yi ta bisa mutunci da girmamawa da  moriyar juna, la’akari da irin lokaci da kalubale da wahalhalun da ta jure har ma da sauran dimbin damarmakin da take da su. (Fa’iza Mustapha)