logo

HAUSA

Hira Tsakanin Shugaba Da Jama’a Ta Shaida Yadda Yake Ba Rayuwarsu Muhimmanci

2021-08-24 11:26:17 CRI

Hira Tsakanin Shugaba Da Jama’a Ta Shaida Yadda Yake Ba Rayuwarsu Muhimmanci_fororder_0824-1

Tun bayan taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta Sin karo na 18, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ziyarci wurare daban daban kamar yankin ciyayi ko yankin duwatsu ko kauyuka, tare da tattaunawa da jama’ar kananan kabilu sau da dama. Shugaba Xi Jinping yana maida hankali sosai kan yanayin rayuwar jama’a da ra’ayoyinsu baki daya.

A watan Nuwanban shekarar 2013, shugaban kasar Sin Xi Jinping wanda ke ziyara a lardin Hunan ya ziyarci kauyen Shibadong na kabilar Miao dake yammacin lardin don gaida mazaunan kauyen. A yayin da shugaba Xi ya ziyarci gidan wata tsohuwa Shi Pazhuan mai fama da talauci a kauyen, Shi Pazhuan ba ta san wannan bako shugaba ne ba, ta tambayi shi, shin wane ne kai? A cikin hirarsu, shugaba Xi ya maida tsohuwa Shi tamkar ‘ya.

Shugaba Xi ya ce, “Ke kamar ‘yata ce, ina son gaida ki.” Tsohuwa Shi ta ce, “Yau ina farin ciki da ganinka, kai babban shugaba ne, shugaba mai  lura da jama’a.” Shugaba Xi ya ce, “Ni mai hidimtawa jama’a ne.”

A shekarar 2017, aka kawar da talauci daga dukkan kauyen Shibadong, inda kuma aka samu babban sauyi a kauyen. Tsohuwa Shi ta bude karamin kantin sayar da nama da tufaffin gargajiya na kabilar Miao a gaban gidanta, inda take zaman rayuwa na jin dadi. Hirar da ta yi da shugaba Xi ta samu karbuwa sosai a kauyen.

A yayin manyan taruka biyu da aka gudanar a shekarar 2016, shugaba Xi Jinping ya yi hira da wakiliyar kabilar Tibet kuma likitar asibitin kula da lafiyar haihuwar mata na lardin Qinghai Niang Maoxian.

Malama Niang ta ce, “Yanzu akwai dakin kiwon lafiya.” Shugaba Xi ya yi mata tambaya cewa, “Akwai yankuna masu fadi a lardin Qinghai, ta yaya makiyaya ke ganin likita?” Malama Niang ta amsa, “Akwai motocin likitoci dake zuwa garuruwa da kauyuka don samar da hidimar likitanci.”

Shugaba ya yi tambayoyi kuma Niang Maoxian ta amsa daya bayan daya.

A shekarar 2019, bayan da shugaba Xi Jinping ya gama sauraron jawabin da wakilin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin na kabilar Mongoliya kuma makiyayi Wu Yunbo ya gabatar, shugaba Xi ya sa kaimi gare shi da ya jagoranci makiyaya a garinsu don sayar da kayayyakinsu masu alamar musamman. Kuma shugaba Xi ya yi masa tambaya kan hanyar zuwa garinsu.

Shugaba Xi ya tambaye shi, “Ina ne hanyar zuwa Gacha?” Malam Wu ya amsa, “Kana iya zuwa Gacha ta hanyar bin jirgin sama ko jirgin kasa ko ta mota.” Shugaba Xi ya ce, “Sai ka nuna mini hanyar.” Malam Wu ya ce, “Ka tashi daga birnin Beijing zuwa filin jiragen sama na Tongliao ta jirgin sama, … za mu karbe ka a can.”

Shugaba Xi ya tambayi hanyar ne domin yana maida hankali kan wuraren da jama’ar kananan kabilu ke zaune a yankin.

A ranar 11 ga watan Febrairun shekarar 2018, shugaba Xi ya ziyarci gidan Jihaoyeqiu mai fama da talauci a kauyen Sanhe dake garin Zhaojue na lardin Sichuan, yarinya Jihaoyouguo mai shekaru 10 da haihuwa ta rera wata waka da ta koya a makaranta a gaban shugaba Xi, wadda ta burge shi sosai. Shugaba Xi ya yaba mata, tare da yi wa dukkan iyalanta kyakkyawan fata.

Shugaba Xi ya ce, “Ina jin farin ciki sosai da ganin kuna jin dadin zaman rayuwarku. Ina fatan yara za su girma cikin koshin lafiya, da jin dadin zaman rayuwarsu a nan gaba.”(Zainab)