logo

HAUSA

Mounkaila Abdoul Kader: Ina kira ga matasan Afirka su maida hankali kan karatu da aiki

2021-08-24 14:26:07 CRI

Mounkaila Abdoul Kader: Ina kira ga matasan Afirka su maida hankali kan karatu da aiki_fororder_微信图片_20210819160811

Malam Mounkaila Abdoul Kader, wani dan Jamhuriyar Nijar ne wanda a yanzu haka yake karatun digiri na uku a fannin ilimin gona a cibiyar nazarin kimiyyar aikin gona ta kasar Sin. A yayin zantawarsa da Murtala Zhang, Abdoul ya bayyana ra’ayinsa kan ci gaban fasahohin aikin gona na kasar Sin, da bambancin yanayin karatu tsakanin kasarsa Jamhuriyar Nijar da kasar Sin.

Mounkaila Abdoul Kader: Ina kira ga matasan Afirka su maida hankali kan karatu da aiki_fororder_微信图片_20210819160825

Abdoul wanda ke jin dadin rayuwa da karatu a nan kasar Sin, ya kuma yi kira ga matasan Afirka, su kara maida hankali kan harkokinsu na karatu da aiki, saboda a cewarsa, idan aka yi sakaci da harkar karatu da aiki, ba za’a samu ci gaba mai dorewa ba. (Murtala Zhang)