logo

HAUSA

Sin ta bayar da gudunmawar riga-kafin COVID-19 dubu 300 ga Habasha

2021-08-24 10:06:37 CRI

Sin ta bayar da gudunmawar riga-kafin COVID-19 dubu 300 ga Habasha_fororder_0824-A2-Habasha

A safiyar jiya Litinin kasar Habasha ta karbi gudunmawar alluran riga-kafin COVID-19 guda 300,000 daga gwamnatin kasar Sin.

Jakadan kasar Sin a Habasha Zhao Zhiyuan, da ministar lafiyar kasar Habasha Lia Tadesse, da kuma ministan ilmin Habashan Getahun Mekuria ne suka karbi alluran riga-kafin na COVID-19 a filin jirgin saman kasa da kasa na Bole dake Addis Ababa.

Tadesse ta fadawa ’yan jaridu cewa, a wannan rana sun amshi kaso na uku na gudunmawar alluran riga-kafi 300,000 na kamfanin Sinopharm, wadanda za su yi matukar taimakawa kokarin da gwamnatin kasar ke yi na dakile yaduwar annobar COVID-19 a kasar.

Jakadan Sin a Habasha Zhao Zhiyuan, ya ce kawo yanzu, kasar Sin ta samar da alluran riga-kafin COVID-19 kusan miliyan guda ga kasar Habasha da nufin tallafawa kokarin sashen lafiyar kasar ta gabashin Afrika. (Ahmad)