logo

HAUSA

Ya kamata Amurka ta yankewa kanta hukunci da farko game da batun safarar mutane

2021-08-24 14:27:12 CRI

Ya kamata Amurka ta yankewa kanta hukunci da farko game da batun safarar mutane_fororder_sharhi-hoto

Ranar 23 ga watan Agusta, ranar “tunawa da kawar da manufar safarar bayi bakaken fata” ce da MDD ta tsara. Amma, abin da ya bata ran jama’a shi ne, kwanan baya, kasar Amurka wadda ta saba da “safarar mutane” ta fidda wani rahoto kan safarar mutane na shekarar 2021, inda ta mai da kanta a matsayi ta farko, cikin jerin masu kwarewa wajen hana safarar mutane.

Safarar bayi bakaken fata laifi ne na ‘yan mulkin mallaka, wanda bai kamata a manta da shi ba. Amma, abin bakin ciki shi ne, kasar Amurka ta saka ra’ayin wariyar launin fata cikin halayen jama’arta bayan cinikin bayin da ta yi cikin zamanin da, lamarin da ya sa, da kar aka kawar da ra’ayin wariyar launin fata a kasar Amurka.

Ya zuwa yanzu, ana ci gaba da fama da matsalar safarar mutane da tilastawa mutane yin aiki cikin kasar Amurka, lamarin da ya haifar da matsala ga tsirarrun al’ummun kasar. Kuma, yawan mutanen da aka aikata musu wannan laifi da muka sani ya zama kadan daga cikin ainihin yawansu.

Abubuwan keta hakkin dan Adam da kasar Amurka ta yi, sun bata “sanarwar ‘yancin kai” ta kasar, ya dace kasar Amurka ta yankewa kanta hukunci bisa laifin keta hakkin dan Adam da ta aikata, a maimakon tsoma baki cikin harkokin sauran kasashen duniya. (Maryam)