logo

HAUSA

‘Yan bindiga sun kashe mutane 9 a arewa maso yammacin Najeriya

2021-08-23 20:46:34 CRI

Rahotanni daga Najeriya na cewa, wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba, sun kashe mutane 9 a wani kauye a jihar Kaduna dake yankin arewa maso yammacin kasar mai fama da tashin hankali a karshen mako.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, an kai harin na ranar Asabar ne, a Ungwan Dooh, wani kauye a yankin Zangon Kataf a jihar ta Kaduna. Ya bayyana cewa, sojoji sun amsa kiran neman taimakon gaggawa daga mazauna wurin, inda suka garzaya yankin, sai dai maharan sun arce yayin da suka ga sojojin na zuwa.

Aruwan ya ce, yawan mamata na iya karuwa, yayin da aikin nema da ceto dake gudana, ka iya kaiwa ga gano karin wadanda harin ya shafa.