logo

HAUSA

Sharhi: Ya kamata Amurka ta warke daga “ciwon tsoron kasar Sin”

2021-08-23 20:20:03 CRI

Sharhi: Ya kamata Amurka ta warke daga “ciwon tsoron kasar Sin”_fororder_e1fe9925bc315c60a17e0b403bb6301b48547742

Kwanan baya, sabon sakataren rundunar sojan sama na Amurka Frank Kendall ya bayyana cewa, burin da yake son cimmawa shi ne kirkiro fasahohin zamani da za su “tsoratar da kasar Sin”, misalin shirin da yanzu haka rundunar sojan sama ke aiwatarwa na kara inganta jirgin saman yaki samfurin F-35 da ba a iya ganinsa.

Kasancewarsa tsohon sojan kasa wanda ya yi rayuwa a zamanin yakin cacar baka, ya sa ra’ayin yakin cacar baka ya shiga ran Frank Kendall, kuma har yanzu akwai ‘yan siyasar Amurka da yawa da ke rungumar ra’ayin, kuma abin da suke kira “tsoratar da kasar Sin” a hakika ya shaida yadda su kansa ke jin tsoron bunkasuwar kasar Sin. Sai dai irinsu Frank Kendall ba su fahimta ba, kasar Sin ba za ta maye gurbin Amurka ba, Amurka za ta iya kara bunkasa, kuma kasar Sin a nata bangaren ma tabbas za ta samu karin ci gaba.

A hakika, Amurka ta dade tana fama da “ciwon tsoro”. A shekarun 1980, Amurka ta kamu da “ciwon tsoron Japan”. A lokacin, alkaluman GDP din kasar Japan ya kusan kai kaso 70% na kasar Amurka, kafin daga bisani Amurka ta tilasta Japan din ta sa hannu kan yarjejeniyar Plaza, matakin da ya sa darajar kudin Japan ta karu, wanda har ya sa tattalin arzikin Japan ya tabarbare.

A cikin ‘yan shekarun baya kuma, wasu gungun Amurkawa da na yammacin duniya ma ba su ji dadin saurin bunkasuwar kasar Sin, musamman ma Amurka ba ta son ganin bunkasuwar kasar Sin da ma yadda kasar ta zarce ta a wasu fannoni, sabo da a ganinta, hakan babbar barazana ce gare ta. Don haka, wasu ‘yan kasar sun yi ta yayata furucin nan na wai “kasar Sin barazana ce”, a yunkurinta na mai da kasar saniyar ware da ma dakile ta.

Lalle ya kamata Amurka ta warke daga “ciwon tsoron kasar Sin”, sabo da kasar Sin ba ta da niyyar maye gurbin wata kasa.

Na farko, duk da cewa gibin da ke tsakanin Sin da Amurka ta fannin karfin tattalin arziki na raguwa, amma har yanzu Amurka kasa ce mafi karfin tattalin arziki a duniya, musamman ma idan an kwatanta kasashen biyu ta fannin kudin shigar da kowane dan kasar ke samu. Baya ga haka, har yanzu, Amurka tana sahun gaba ta fannoni da dama, ciki har da soja da kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha. Ko da ma kasar Sin ta zarce Amurka ta fannin karfin tattalin arziki bayan wasu shekaru, lalle ba za a iya dauka cewa kasar Sin ta zarce Amurka, sabo da ba a iya auna karfin wata kasa bisa tattalin arziki kawai ba. Kuma ko da kasar Sin ta kara bunkasa, ba lalle ba ne ta kawo barazana. Kamar yadda kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Madam Hua Chunying ta ce, “Dabbar Panda tana da girma, amma da gaske ne ta fi shaho hadari?”

Na biyu kuma, al’adar Sinawa ce su zauna lafiya da sauran al’ummu. Kasar Sin ba ta da niyyar maye gurbin wata ko yin babakere a duniya, kullum tana martaba manufar zaman lafiya da hadin gwiwa da kasashen duniya, ba ta ko taba ta da yaki kan wata kasa ba, kuma ba ta taba tsoma baki a harkokin cikin gida na wata kasa ba. Baya ga haka, ba ta taba mamaye filaye na wata kasa ba, ko kuma ta sanya takunkumi kan wata kasa. Abin da take son gani shi ne, a yi hadin gwiwar cin moriyar juna, kuma shawarar ziri daya da hanya daya da ta gabatar ta shaida hakan.

Na uku, kullum kasar Sin na martaba ‘yancin al’ummun kasashe daban daban na zabar hanyoyinsu mabambanta, kuma ba ta son tilasta sauran kasashen duniya su yarda da tsarinta, balle ma ta haifar da kiyayya a tsakanin kasa da kasa. A kasashe masu tasowa da dama, Sinawa na gina gadoji da hanyoyi, kungiyoyin ma’aikatan lafiya da kasar Sin ta tura kasashen Afirka ma sun shafe shekara da shekaru suna samar da gudummawar jiyya ga al’ummar Afirka, amma kasar Sin ba ta ko taba gindaya sharudan siyasa ga kasashen ba.

A game da furucin Mr. Frank Kendall, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Madam Hua Chunying ta mayar da martanin cewa, ya kamata Mr.Kendall ya tambayi rundunar sojan saman kasar Sin ko sun yarda ko a’a.

Kamar yadda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana, “al’ummar kasar Sin ba su son ta da rikici, amma kuma ba za su ji tsoro ba idan rikici ya taso, kuma ba za ta sukunya ba duk matsala da hadari da ke gabanta.”

Kasar Sin ba ta da niyyar kalubantar wata kasa ko yanki, amma kuma ba ta jin tsoron kalubalen da wata kasa ta tayar mata. (Lubabatu Lei)