logo

HAUSA

Babu wanda da za a bar su a baya cikin aikin kawar da talauci

2021-08-23 14:10:54 CRI

Babu wanda da za a bar su a baya cikin aikin kawar da talauci_fororder_hoto

A bana, kasar Sin ta cimma nasarar fatattakar talauci daga fadin kasar, kana, ta fara aikin neman wadatar al’umma bisa dukkanin fannoni. Yadda aka taimakawa al’ummomin kananan kabilu, wadanda suke zaune a yankunan karkara kawar da talauci, da kuma neman wadata cikin hadin gwiwa, yana jan hankalin shugaban kasar Sin Xi Jinping.

Dangane da wannan batu, ga Karin bayani daga Maryam Yang…

Garin Dulongjiang yana gundumar Gongshan ta jihar Nujiang dake lardin Yunnan na kasar Sin, kuma daya ne daga cikin wasu kebabun wurare na  kasar Sin. Galibin lokaci a shekara daya, kusan babu mutanen da suke iya shiga garin, bisa yadda kankara suka kange tsaunukan dake kewayensa. Shi ya sa, a kan kira garin da suna “gari mai sa mutane zubar da hawayensu”. Kana, kabilar Dulong dake zama a garin, daya ce daga cikin kananan kabilun da suka fi karancin al’umma a kasar Sin.

A farkon shekarar 2014, wasu jami’an garin suka aikawa shugaba Xi Jinping wata wasika, inda suka bayyana murnar bude hanyoyi a cikin garin, sa’an nan kuma, shugaba Xi Jinping ya amsa wasikarsu, inda shi ma ya taya su murna. Daga bisani kuma, a shekarar 2015, aka gayyaci matanen garin Dulong zuwa wurin da shugaba Xi Jinping ke zaune a lokacin da yake ziyarar aiki a lardin Yunnan. A yayin ganwarsu, Xi Jinping ya ce,“Yawan al’ummomin kabilar Dulong ba shi da yawa, kamar akwai mutane 6900, amma, kabilar Dulong daya ce daga cikin kabilu 56 na kasar Sin. A halin yanzu, dukkanmu muna da nauyin farfado da kasarmu cikin hadin gwiwa, domin cimma burikanmu, kuma ba za a bar kabila ko daya ba cikin aikin neman wadata bisa dukkan fannoni. Jam’iyyar Kwaminis ta Kasar Sin tana mai da hankali kan dukkanin kabilun kasar, tana kuma fatan dukkan al’ummomin kabilu daban-daban za su sami wadata cikin hadin gwiwa, kuma JKS da gwamnatin kasa za su goya musu baya a ko da yaushe.”

Cikin farkon rabin shekarar 2019, lardin Yunnan ya sanar da fitar da kananan kabilu uku da suka hada da kabilar Dulong, da kabilar Jino, da kuma kabilar De’ang daga kangin talauci. Kuma, a ranar 10 ga watan Afrilun wannan shekara, Xi Jinping ya sake aika wasika ga al’ummomin garin Dulong, inda ya taya su murnar kawar da talauci baki daya, da kuma sa kaimi gare su don su ci gaba da dukufa wajen kyautata zaman rayuwarsu.

Bayan cikakken zaman taron wakilan JKS karo na 18 da aka yi a shekarar 2012, Xi Jinping ya ziyarci wurare da dama, inda al’ummomin kananan kabilu suke rayuwa. Ya ziyarci wuraren ba tare da la’akari da nisansu ba, domin kara fahimtar yadda ake aiwatar da manufofin tallafawa al’ummomin kananan kabilu, da kuma yanayin zaman rayuwarsu.

A watan Afrilun shekarar 2014, Xi Jinping ya kai ziyara gidan Abdukeyoumu Rouzi dan kabilar Uygur, dake yankin Kashgar na jihar Xinjiang, domin gane wa idanunsa yadda shi da iyalinsa suke rayuwa. Ya ce,“Dalilina na kawo ziyara a wannan karo shi ne, ina son duba ko manufofin da kwamitin tsakiya ya tsara sun dace da bukatun al’umma, da kuma fatansu. Ya kamata JKS ta tsara dukkanin manufofi, bisa bukatun al’umma, da kuma tallafa musu yadda ya kamata.”

Kabilar Hezhe ita ma daya ce daga cikin kabilun da suka fi karancin al’umma. Al’ummomin kabilar suna rayuwa da aiki ne a yankin dake kusa da kogin Songhua, da kogin Heilong da kuma kogin Wusuli. A watan Mayun shekarar 2016, Xi Jinping ya kai musu ziyara a kauyen Bacha na birnin Tongjiang. Yayin ganawarsu, Xi Jinping ya ce,“Wannan shi ne karo na farko da na zo wurin da al’ummomin kabilar Hezhe ke zama, na ji dadi sosai. Kamar yadda aka rera cikin wakar “jiragen ruwa a kan kogin Wusuli”, cewar, jiragen ruwan dake kan kogin na cike da kifaye, ya nuna ingancin zaman rayuwar al’ummomin kasar Sin. Ba za a bar wani a baya ba cikin aikin neman wadata. Ina mai da hankali kan dukkan al’ummomin kabilu daban daban na kasar Sin, ya kamata mu hada kanmu, domin neman ci gaban kasa baki daya.” (Mai Fassarawa: Maryam Yang)