logo

HAUSA

Masanan kasa da kasa sun gargadi siyasantar da asalin COVID-19 cewa ba zai haifarwa duniya da mai ido ba

2021-08-23 19:36:20 cri

Masanan kasa da kasa sun gargadi siyasantar da asalin COVID-19 cewa ba zai haifarwa duniya da mai ido ba_fororder_微信图片_20210823193305

Hankulan kwararru da masanan kasa da kasa na kara karkata wajen yin tsoka, fashin baki, har ma da yin gargadi game da sanya siyasa da shaguban da wasu ’yan siyasa na kasashen yammacin duniya ke yiwa batun binciken asalin annobar COVID-19. Koda a karshen makon da ya gabata ma, wani kwararren masani daga tarayyar Najeriya ya yi gargadin cewa, siyasantar da batun aikin binciken gano asalin cutar COVID-19 ba zai taimaka wajen dakile annobar ba, kana zai iya gurgunta hadin gwiwar kasa da kasa wajen tsara dabarun hana faruwar barkewar wata annobar a nan gaba. Charles Onunaiju, daraktan cibiyar nazarin al’amurran kasar Sin dake Abuja a Najeriya, ya wallafa wani sharhi a jaridar Vanguard da ake wallafawa a kasar, inda ya bayyana cewa, duk da kasancewar masana kimiyya sun bayyana cewa mai yiwuwa ne cutar COVID-19 ta samo asali ne daga indallahi ba daga dakin gwaje-gwaje ba, amma abin takaici duk da hakan, sai ga shi gwamnatin kasar Amurka tana ci gaba da jirkita batun asalin cutar wanda binciken masana kimiyya ya tabbatar, sannan kasar tana ta kokarin siyasantar da batun da kuma mayar da shi tamkar wani batu na yakin cacar baka don shafawa kasar Sin kashin kaza. Masanin ya bukaci a koma kan turbar binciken masana maimakon yin shaci fadi, kasancewar zarge-zarge bashi da wani alfanu kuma ba zai taimakawa hadin gwiwar kasa da kasa wajen kandagarkin hana yaduwar wata annobar a nan gaba ba. Onunaiju ya ce, yayin da ake yada zarge zarge game da batun asalin cutar da kuma zargin kasar Sin da rashin bayyana lamarin a fili, ta bayyana a fili cewa, zarge zargen da Washington ke yi tamkar wani salo ne na boye gazawarta wajen dakile cutar da kuma magance ta. Koda yake, ba wai mista Onunaije ne kadai ke da wannan ra’ayi ba, ita ma jaridar Herald da ake wallafawa a kasar Zimbabwe, ta ce Amurka na fakewa da batun binciken gano asalin cutar COVID-19 domin cimma muradun siyasa. Makalar da jaridar ta wallafa a karshen mako ta ambato cewa, kamata ya yi kasashen duniya su nuna kin amincewa da siyasantar da batun binciko asalin wannan cuta, kuma hadin gwiwar sassan kasa da kasa ne kadai, zai tabbatar da nasarar yaki da wannan annoba. A wani ci gaban kuma, ita ma jaridar Singapore Straits Times, ta ce a baya bayan nan an samu adadin mutane har 1,000 da cutar COVID-19 ta hallaka a kwana daya kawai a Amurka. Kaza lika a tsakanin wata guda, matsakaicin adadin masu mutuwa a duk rana a kasar ya kai mutum 769, wanda shi ne adadi mafi yawa da kasar ke samu, tun daga tsakiyar watan Afirilu. Kukan kurciya dai an ce jawabi ne mai hankali ne kadai ke ganewa. (Ahmad Fagam)