logo

HAUSA

Raya kasuwar cikin gida da ta waje tare zai taimaka ga samar da makoma mai haske ga Hong Kong

2021-08-23 20:46:11 CRI

Raya kasuwar cikin gida da ta waje tare zai taimaka ga samar da makoma mai haske ga Hong Kong_fororder_A

Daga yau Litinin zuwa jibi Laraba, wata babbar tawaga dake kunshe da jami’ai daga ofishin kula da harkokin yankunan Hong Kong da Macau na majalisar gudanarwa ta kasar Sin, da hukumar raya kasa da yin kwaskwarima ta kasa, da ma’aikatar kimiyya da fasaha, gami da babban bankin kasar Sin, ta je yankin Hong Kong, inda jami’an za su shirya wasu muhimman tarukan fadakar da al’umma game da muhimmancin shirin raya kasa na shekaru biyar karo na 14. Wannan lamarin zai taimaka wa Hong Kong more damammakin ci gaba, tare da bunkasar kasar Sin baki daya.

Shirin shekaru biyar na raya kasar Sin karo na 14, ya jaddada cewa, idan aka mayar da hankali kan raya tattalin arziki a cikin gida, za a iya hade kasuwar cikin gida da ta ketare domin samun ci gaba mai karfi da dorewa. Ya dace yankin Hong Kong ya yi amfani da wannan dabara, a wani mataki na samar da kuzari da zarafi ga ci gabansa.

Raya kasuwar cikin gida da ta waje tare zai taimaka ga samar da makoma mai haske ga Hong Kong_fororder_B

Kasar Sin tana kara maida hankali kan samar da ci gaba a cikin gida, da kara habaka bukatun cikin gida, al’amarin dake samar da manyan damammakin ci gaba ga yankin Hong Kong.

Har wa yau, kasar Sin tana himmatuwa wajen hade kasuwar cikin gida da ta kasashen ketare, shi ma yankin Hong Kong, na da kwarewa wajen shiga wannan fanni.

Bugu da kari, shirin shekaru biyar na raya kasar Sin karo na 14, ya sake ayyana matsayin Hong Kong, ciki har da inganta muhimmancinsa a matsayin mahadar hanyoyin sufurin jiragen saman kasa da kasa, da cibiyar kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha ta kasa da kasa, da cibiyar inganta musanyar al’adun kasar Sin da na ketare da sauransu. Babu tantama duk wadannan matakan, za su sanyawa Hong Kong sabon kuzarin ci gaba. (Murtala Zhang)