logo

HAUSA

Mutum guda ya mutu wasu daruruwa sun kauracewa gidajensu sakamakon ambaliyar ruwa a arewacin Ghana

2021-08-22 16:58:45 CRI

Mummunar ambaliyar ruwa a yankin Upper West dake arewacin kasar Ghana ta yi ajalin mutum guda kana ya raba wasu daruruwan mutanen da muhallansu, kamar yadda jami’ai suka tabbatar da hakan.

Ahmed Mustapha, jami’in hukumar yaki da bala’u ta kasa (NADMO), na shiyyar, ya sheda wa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, wata mace ‘yar shekaru 80 da haihuwa ta mutu sannan wasu unguwanni 19 ambaliyar ruwan ta malale bayan sheka ruwan sama kamar da bakin kwarya a ranar Juma’a.

Mustapha yace, a kalla mutane 323 sun kauracewa muhallansu bayan da ambaliyar ruwan ta lalata gidaje 101 a shiyyar Wa East, kuma har yanzu ana cigaba da tantance barnar da ambaliyar ta haifar.

Yace hukumar ba da agaji ta Red Cross dake Ghana ta tuntubi hukumar NADMO tare da yin alkawarin bayar da tallafi ga mutanen da bala’in ya rutsa da su.(Ahmad)