logo

HAUSA

An shirya taron karawa juna sani kan shawarar ziri daya da hanya daya a Najeriya

2021-08-21 16:05:23 CRI

An shirya taron karawa juna sani kan shawarar ziri daya da hanya daya a Najeriya_fororder_1

Ofishin jakadancin kasar Sin dake tarayyar Najeirya, ya shirya taron karawa juna sani mai taken “inganta shawarar ziri daya da hanya daya, tare da karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da Najeriya” da hadin gwiwar ma’aikatar kula da matasa da wasannin ta kasar Najeriya da kuma cibiyar yada al’adun kasar Sin.

Yayin taron, jakadan kasar Sin Cui Jianchun ya yi bayani kan asalin shawarar ziri daya da hanya daya, da sakamakon da aka samu bayan kasashen duniya sama da dari daya sun shiga shawarar. Ya kuma bayyana cewa, a cikin shekaru takwas da suka gabata, shawarar ziri daya da hanya daya ta samar da damammakin samun ci gaba ga kasashe da dama wadanda suka shiga shawarar, ciki har da Najeriya.

Game da kayayyakin more rayuwar jama’a da kasar Sin ta taimaka wajen ginawa a Najeriya, jakada Cui ya bayyana farin ciki matuka, inda ya ce, a cikin watannin da suka gabata, ya halarci bikin kaddamar da layin dogon da ya hada Legos da Ibadan, da bikin kaddamar da layin dogo da ya hada Kaduna da Kano.

Jakada Cui ya kara da cewa, Sinawa su kan bayyana cewa, idan ana son samun wadata, dole ne a gina hanya, a don haka muhimman layukan dogon da aka gina za su samar da guraben aikin yi ga al’ummun Najeriya a nan gaba, haka kuma za su taka rawa kan ci gaban tattalin arzikin kasar, lamarin da ya shaida cewa, Najeriya ta ci gajiya daga shawarar ziri daya da hanya daya.

A karshe dai jakada Cui ya yi bayani kan manufofin hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Najeriya a fannoni daban daban a nan gaba, kuma ya bayyana fatansa ga matasa cewa, su ne fatan al’umma ne, kuma makomar kasa, inda ya yi fatan za su hada kai domin samar da makoma mai kyau ga hadin gwiwar moriyar juna dake tsakanin kasashen biyu wato Sin da Najeriya a cikin shekaru hamsin masu zuwa.(Jamila)