logo

HAUSA

Sharhi: Me ya sa Amurka ta ci tura wajen wanzar da tsarin dimokuradiyyarta a Afghanistan

2021-08-20 14:16:31 CRI

Sharhi: Me ya sa Amurka ta ci tura wajen wanzar da tsarin dimokuradiyyarta a Afghanistan_fororder_2

A ranar 16 ga wata, shugaban kasar Amurka Joe Biden, ya bayyana cewa, aikin da Amurka ta gudanar a kasar Afghanistan, shi ne yaki da ta’addanci a maimakon farfado da kasa, da ma wanzar da dimokuradiyya. Sai dai furucin bai iya boye yadda Amurka ta ci tura wajen wanzar da tsarin dimokuradiyyar ta a kasar ba.

Masani ilmin siyasa na kasar Afghanistan Matiullah Kharoti ya yi nuni da cewa, Amurka ta tura matasan Afghanistan da dama zuwa kasashen yamma, don a ilmantar da su bisa tsarinsu, kafin daga bisani su koma Afghanista su gudanar da mulkin kasar. Amma ko kadan matasan ba su fahimci halin da kasarsu ke ciki ba, balle sanin wahalar da talakawan kasar ke fuskanta.

Sharhi: Me ya sa Amurka ta ci tura wajen wanzar da tsarin dimokuradiyyarta a Afghanistan_fororder_1

Ya kara da cewa, a hakika, yadda Amurka ta tilasta wanzar da dimokuradiyya salon kasashen yamma, amma ba tare da kula da bukatun al’ummar kasar na samun kwanciyar hankali da ci gaba ba, ya sa da wuya su hada kawunan al’umma, matakin da ya sa “gwamnatin dimokuradiyya” ta wargaje a karshe.

Dan jaridar kasar Afghanistan Abdul Taimoor yana ganin cewa, tabbas Amurka za ta ci tura wajen wanzar da tsarin dimokuradiyyarta a Afghanistan, wadda ta sha bamban sosai da kasashen yammacin duniya ta fannonin siyasa, da tattalin arziki, da zaman al’umma da ma al’adu.

Shi kuwa Muhammad Yusuf Rahnaward, shugaban cibiyar nazarin hanyar siliki ta Afghanistan ya ce, “ina ganin Amurka ta cuci ‘yan kasarmu cikin shekaru 20 da suka wuce. Abin lura shi ne, abin da ta fada ya sha bamban da matakan da ta dauka. Amurka na iya yin watsi da gwamnatin Afghanistan, duk lokacin da ta ga bukatar hakan ta taso.”