logo

HAUSA

Sin na ci gaba da taka rawa kan farfadowar tattalin arzikin duniya

2021-08-20 20:01:32 CRI

Sin na ci gaba da taka rawa kan farfadowar tattalin arzikin duniya_fororder_sin

A halin yanzu nau’in kwayar cutar COVID-19 na Delta yana bazuwa a fadin duniya, lamarin da ya illata farfadowar tattalin arzikin duniya, a karkashin irin wannan yanayi, sabbin alkaluman tattalin arzikin da gwamnatin kasar Sin ta fitar sun yi matukar jawo hankalin al’ummun kasa da kasa.

An lura cewa, a watan Yulin da ya gabata, wasu alkaluman tattalin arzikin kasar Sin sun sauka, sakamakon karuwar dalilai marasa tabbaci, wadanda suke shafar kasashen waje, da hadarin ambaliyar ruwa a gida, da tasirin yaduwar annobar COVID-19 a wasu sassan kasar, amma a takaice dai tattalin arzikin kasar yana ci gaba da farfadowa kamar yadda yake a baya.

Da farko, zuba jari a kasashen waje, da samun jarin waje a kasar Sin, suna gudana yadda ya kamata, wanda hakan ya ingiza farfadowar tattalin arzikin duniya. A sa’i daya kuma, jarin da kasar Sin ta zuba a kasashen waje, shi ma yana taimakawa wajen farfado da tattalin arziki a wuraren, kuma kamfanonin kasar Sin suna taka babbar rawa, wajen samar da kayayyaki domin biya bukatun kasuwar duniya, wadda ke gamuwa da matsala sakamakon yaduwar annobar. Kana abun farin ciki shi ne, har kullum, kasar Sin tana bude kofa ga ketare, ta yadda za ta ba da gudummowa kan farfadowar tattalin arzikin duniya a kan lokaci.

Hakika kasar Sin tana ci gaba da ingiza farfadowar tattalin arzikin duniya, haka kuma tana ingiza cudanyar tattalin arziki dake tsakanin kasa da kasa a fadin duniya. (Jamila)