logo

HAUSA

Jakadan Sin ya bukaci a kara kokarin yaki da ta’addanci a Afghanistan

2021-08-20 10:04:55 CRI

Jakadan Sin ya bukaci a kara kokarin yaki da ta’addanci a Afghanistan_fororder_210820-ahmad-1-MDD

Jakadan kasar Sin ya bukaci a cigaba da kara azama domin yakar ayyukan ta’addanci a kasar Afghanistan domin hana kasar ta sake zama wata matattarar ’yan ta’adda.

A shekaru 20 tun bayan kaddamar da fara yaki da ta’addanci a kasar Afghanistan, ba a cimma nasarar kawar da barazanar ta’addanci ba. A maimakon hakan, kungiyoyin ta’addanci a kasar sun sake karuwa daga ’yan tsiraru zuwa sama da guda 20 yayin da aka samu ’yan ta’addan sama da 10,000 daga kasashen waje, Dai Bing, mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin a MDD ya bayyana hakan.

Tawagar masu sa ido na kwamitin sulhun MDD sun sha fiddar rahotanni a wannan shekarar, inda suka bayyana cewa kungiyoyin ta’addanci, kamar su ISIS, al-Qaida, ETIM, da kuma Pakistani Taliban sun yadu, kana sun samu gindin zama a Afghanistan, ya bayyana hakan ne ga kwamitin sulhun MDD.

Dai ya yi gargadin cewa, halin da ake ciki a yanzu a kasar Afghanistan ya haifar da manyan sauye-sauye, kuma mai yiwuwa ne kungiyoyin ’yan ta’addan su yi amfani da wannan damar ta tashin hankalin kasar. (Ahmad Yaya)