logo

HAUSA

Sojojin Mali 11 sun mutu a harin da aka kai musu

2021-08-20 11:19:29 CRI

Rundunar sojojin kasar Mali ta sanar a jiya Alhamis cewa, wasu sojojinta 11 sun halaka sakamakon harin da aka kai musu a wannan rana a tsakiyar kasar.

Bayanan da rundunar sojin Mali ta wallafa a shafinta na yanar gizo ya yi nuni da cewa, an kai harin mota ga ayarin motoci na wasu sojojinta da ke gudanar da aikinsu a yankin Mopti da ke tsakiyar kasar, kafin daga bisani wasu dakarun da ba a san ko su wanene ba sun harbe da bindiga, harin wanda ya yi sanadiyyar mutuwar sojoji 11, a yayin da wasu 10 suka jikkata.

Rundunar sojin Mali ta ce, ana kula da sojojin da suka jikkata yadda ya kamata. A yanzu haka kuma, babu wanda ya sanar da daukar alhakin harin. (Lubabatu)