logo

HAUSA

Kafar yada labaran Zimbabwe: Ya kamata Afrika ta yi watsi da batun siyasantar da asalin cutar COVID-19

2021-08-19 10:39:10 CRI

Kafar yada labaran Zimbabwe: Ya kamata Afrika ta yi watsi da batun siyasantar da asalin cutar COVID-19_fororder_210819-Ahmad2-Herald

Afrika, a halin yanzu tana fama da karancin alluran riga-kafin COVID-19, kuma ya kamata nahiyar ta hada kai da kasar Sin domin neman mafita game da illolin dake tattare da annobar, kamar yadda sharhin jaridar Herald ta kasar Zimbabwe ta wallafa a ranar Laraba ya bayyana.

A cewar sharhin, tilas ne nahiyar ta yi watsi da matsin lambar da Amurka take yi a halin yanzu inda take dora alhaki kan kasar Sin game da tushen annobar kuma a maimakon haka kamata ya yi a kara karfafa hadin gwiwar kasa da kasa domin lalibo hanya mafi dacewa don kawar da annobar.

A cewar sharhin, cece-kuce kan batun asalin cutar da Washington ke yi wata manufar siyasa ce da nufin kawar da hankalin al’ummar duniya game da hakikanin yaki da abokiyar gaba ta hakika wato annobar.

Ta kara da cewa, batun binciken asalin cutar wata makarkashiya ce ake shiryawa domin shafawa kasar Sin bakin fenti wanda bai dace ba, kuma matakin zai kara lalata shirin da duniya ke yi na yaki da annobar.

Sharhin ya ce kasar Zimbabwe ta yi kokari matuka wajen dakile bazuwar annobar, ta danganta nasarorin da ta samu kan hadin gwiwar kut-da-kut da kasar ta yi da Sin.

Sharhin ya kara da cewa, hadin gwiwar kut da kut tsakanin Zimbabwe da Sin ya baiwa kasar damar zama a sahun gaba a yaki da annobar, kuma babu shakka wannan zai kasance a matsayin wani gagarumin sauyi a Afrika. (Ahmad)