logo

HAUSA

Ba wasu sassan ‘yan aware da za su cimma nasarar gurgunta ci gaban Tibet

2021-08-19 20:26:54 CRI

Ba wasu sassan ‘yan aware da za su cimma nasarar gurgunta ci gaban Tibet_fororder_tibet

A bana ne ake cika shekaru 70, da cimma nasarar ‘yantar da yankin Tibet na kasar Sin cikin lumana. A yau Alhamis ne ake bikin wannan muhimmiyar rana, inda aka yi shagulgula a birnin Lhasa, fadar mulkin Tibet, inda al’ummun jihar mai cin gashin kai, ke cike da farin ciki da manyan sauye sauye da suka gani cikin wadannan shekaru 70.

Cikin sama da shekaru 70 da suka gabata, tarihi ya tabbatar da irin nasarar da aka samu a fannin bude kofofin Tibet. Kuma daga fannin safarar hajoji da a baya ake yi ta hanyar dako a kawunan mutane, da daukar su a bayan dabbobi, zuwa yanayin yanzu da kauyuka ke da titunan mota, da hanyoyin jiragen sama sama da 140 dake sada yankin da sauran sassan kasashen waje. Kaza lika daga tsohuwar jihar Tibet, wadda kaso 90% na al’ummun ta ba su da isasshen abinci da tufafi, zuwa ci gaban da manoma da makiyaya suka samu a bangaren samun kudin shiga cikin shekaru 18 a jere, yankin ya ga manyan sauye sauye.

A baya al’ummar jihar Tibet na kona kashin dabbobi ne domin dumama muhalli, amma a yanzu jihar na da isasshen lantarki, da turakun sadarwa na intenet bisa fasahar 4G. Ko shakka babu tsohuwar Tibet ta sauya a yanzu, yayin da rayuwar al’ummun ta suka yi matukar inganta.

Bayan shekaru 70, al’ummar Tibet sun lura da muhimmancin hadin kai da daidaito a matsayin babban alheri, sun kuma san cewa duk wani mataki na rarrabuwa, ba abun da zai haifar sai asara. Wannan tamkar bitar tarihi ne, kuma alkibla ce ga ci gaban Tibet a nan gaba. Kaza lika ko shakka babu, ba wasu sassan ‘yan aware da za su cimma nasarar gurgunta ci gaban Tibet. (Saminu)