logo

HAUSA

Afghanistan Na Bukatar Goyon Bayan Kasashen Duniya Cikin Yanayin Sauke Da Ta Shiga

2021-08-19 19:43:47 CRI

Afghanistan Na Bukatar Goyon Bayan Kasashen Duniya Cikin Yanayin Sauke Da Ta Shiga_fororder_111

Daga Saminu Alhassan

Yayin da hankula ke karkata ga gagarumin sauyi da ya auku a Afghanistan, don gane da karbe mulki da kungiyar Taliban ta yi a kasar, bayan shekaru 20 ana dauki ba dadi tsakanin dakarun kungiyar, da dakarun gwamnatin da Amurka ke marawa baya, yanzu haka masharhanta da dama na ganin lokaci ne na martaba ra’ayin al’ummar kasar, da baiwa al’ummun Afghanistan damar aiwatar da manufofin da suka zabawa kan su.

Tuni dai wasu kasashe suka fara nuna goyon bayansu ga manufar Taliban, ta kafa gwamantin da al’ummar kasar za ta amince da ita, suna masu alkawarin kare hakkokin al’ummar kasa, da muradun ci gaban ta.

Mafi yawan kasashen dake nuna shakku kan manufofin gwamnatin Taliban a Afghanistan, na la’akari ne da halin da kasar ta shiga shekaru 20 baya, lokacin da kungiyar Taliban din ke rike da madafun ikon ta, a wani yanayi da sassa daban daban suka rika suka da cewa, ya sabawa dokokin kasa da kasa na kare hakkin bil adama, da ’yancin warwalar mata, da rashin kyakkyawar dangantaka tsakanin kungiyar da sauran kasashen duniya.

Bugu da kari, a wancan lokaci, ana kallo Taliban a matsayin kungiyar dake daurewa kungiyoyin ta’addanci gindin cin karen su ba babbaka, har ma an rika zargin cewa, kasar ta zama wani sansani na horas da ’yan ta’adda.

To sai dai kuma a wannan karo, kungiyar Taliban, ta sha alwashin sauya irin wadannan matakai, tare da tabbatar da cewa, manufofin da za ta aiwatar ba za su haifar da barazanar tsaro ga kasashen dake makwaftaka da ita ba. Kana za ta tabbatar da cewa, ba ta haifarwa kan ta makiya na ciki da wajen kasar ba.

Ko shakka babu, irin wadannan kalamai dake fitowa daga bakin masu magana da yawun Taliban, suna da karfafa gwiwa, kuma kafin yanke hukunci kan sahihancin manufofin kungiyar, kamata ya yi sassan kasa da kasa su baiwa kungiyar damar nuna gaskiyar ikirarin ta, game da sabbin manufofin da gwamnatin ta yanzu za ta aiwatar. (Saminu Alhassan)