logo

HAUSA

Inganta ayyukan hukumar dakile cutuka ta Afrika CDC zai taimakawa aikin yaki da annoba

2021-08-19 11:42:59 CRI

Inganta ayyukan hukumar dakile cutuka ta Afrika CDC zai taimakawa aikin yaki da annoba_fororder_210819-Ahmad5-Africa CDC

Akwai bukatar gaggauta karfafa ayyukan hukumar kula da tsarin kiwon lafiyar Afrika domin ta samu damar jure kalubalolin yaki da annobar COVID-19 a nahiyar, wani jami’in hukumar ta Afrika CDC ya bayyana hakan.

Ana bukatar kara zuba jari domin kawo sauye-sauye a tsarin kiwon lafiyar Afrika ta hanyar samar da kwarewa, da sanya ido wajen bibbiyar cutuka, da samar da muhimman kayayyakin gwaje-gwajen lafiya, da muhimman magunguna, Ebere Okereke, babban jami’i mai ba da shawara a hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta Afrika CDC ya bayyana hakan a yayin tattauwa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ta kafar bidiyo a ranar Laraba.

A cewar Okereke, ajandar bunkasa ci gaban Afrika ta AU nan da shekarar 2063 ta gabatar da bukatar kafa ingantaccen tsarin kiwon lafiya a Afrika, da mayar da hankali wajen kandagarkin yaduwar cutuka da samar da ingantattun kayayyakin da ake bukata a fannin kiwon lafiya domin tabbatar da sauye-sauye a nahiyar. (Ahmad)