logo

HAUSA

Matasa na cimma burikansu a yankin Tibet

2021-08-19 14:38:13 CRI

Matasa na cimma burikansu a yankin Tibet_fororder_hoto

A bana ne, aka cika shekaru 70 da ‘yantar da yankin Tibet na kasar Sin cikin lumana. Cikin wadannan shekaru da suka gabata, tattalin arzikin yankin ya samu gagarumin ci gaba. Kudaden shiga na mutanen yankin sun karu cikin sauri, kuma, zamantakewar al’umma da aikin tallafawa al’umma, sun samu kyautatuwa matuka. Bunkasuwar yankin cikin sauri, ta janyo hankulan matasa sosai, ganin yadda suke neman cimma burikansu.

Ga Karin bayani daga Maryam Yang...

“Mun sayi wannan na’ura daga kasar Amurka…”

Luo Song, mai shekaru sama da 30, yana yin bayani kan na’urorin masana’antarsa. A shekarar 2018, ya kafa masana’antar sarrafa barasa da fasahohin zamani a birnin Lhasa, babban birnin yankin Tibet, kuma ita ce, masana’antar sarrafa barasan zamani ta farko da aka kafa a wannan yanki. Masana’antarsa tana yankin Dagze dake gabashin birnin Lhasa, Luo Song ya gane wa idanunsa yadda aka samu bunkasar ababen more rayuwa a kan hanyarsa ta zuwa aiki. Ya ce, “Hanyar dake tsakanin yankin Dagze da babban birnin Lhasa, ba ta da kyau, a lokacin da na fara aiki a nan, musamman idan an yi ruwan sama, akwai ramuka da yawa a kan hanyar. Yanzu, hanyar tana da kyau. A baya, mutanen birnin Lhasa na ganin cewa, yankin Dagze wani wuri ne mai nisa, amma, yanzu, cikin mintoci 20 zuwa 30 za a isa yankin, Ina ganin, wannan babban canji ne.”

Cikin ‘yan shekarun nan, an kafa tsarin sufuri da ya kunshi hanyoyi da layukan dogo da jiragen sama a birnin Lhasa, wanda ya hada sauran biranen yankin Tibet waje guda. Kuma, gaba daya, tsawon hanyoyin da aka gina a birnin ya kai kilomita 5400, ta yadda motocin bas dake sufurin fasinjoji suke zuwa ko ina a birnin.

A sa’i daya kuma, matsakaicin GDP na kowane mutum a birnin Lhasa, da kudin shigar kowane mazauni yankin karkara a birnin, sun zarce matsakaicin matsayi na kasar Sin, kana, kudin shigar kowane mazaunin birane a Lhasa, yana kusa da matsakaicin matsayin kasar. Haka kuma, ana ci gaba da kyautata tsarin tafiyar da harkokin masana’antu a birnin, yayin da harkokin yawon shakatawa, suke bunkasa cikin yanayi mai kyau. Bayanin na nuna cewa, a shekarar 2020, gaba daya, akwai mutane sama da miliyan 20 da suka fito daga gida da wajen kasar, da suka tafi yawon shakatawa a Lhasa, kuma, kudin shiga da birnin ya samu a fannin yawon shakatawa, ya kai RMB biliyan 30.1. Luo Song ya ce, masu yawon shakatawa daga sauran sassan kasar Sin, sun sayi galibin barasa da masana’antarsa ta samar, kuma, yana dukufa wajen raya kasuwanci cikin yankin Tibet. Yana mai cewa, “Kashi 90 bisa dari na odar da na samu, sun zo daga sauran sassan kasar Sin. A nan jihar Tibet, mutane sun fi son sayan barasar gargajiya, ba kamar barasan da kamfanina ya sarrafa ba ne, shi ya sa, wayar da kan al’ummomin yankin game da barasan zamani, zai kasance wani aikin da zan kara mai da hankali a kai.”

Cikin shekaru 70 da suka gabata, kwamitin tsakiya na JKS da majalisar gudanarwar kasar, sun zuba kudi masu dimbin yawa domin kiyaye da yada al’adun gargajiyar jihar Tibet.

Sang Dan Ci Ji mai shekaru 22, ta gama karatunta a fannin harkar watsa labarai da ilmin yada labarai a jami’ar koyon ilmin sufuri ta Shanghai. Ta fara yin karatu a wasu sassan kasar Sin, tun tana makarantar sakandare, yanzu, manyan sauye-sauyen da aka samu a garinta wato birnin Lhasa sun burge ta sosai. Tana mai cewa, “Na ga kantuna da shagunan dake kusa da gidana, na ga bunkasuwar tattalin arzikin birnin matuka, kuma, zaman rayuwar al’umma ya sami kyautatuwa sosai. A lokacin da nake karama, na kan kalli shirye-shiryen al’adun gargajiyar yankin Tibet ta hoton bidiyo kawai, amma, cikin ‘yan shekarun nan, na ga mutane sun fara koyon fasahohin rawa da sauransu a lambunan dake kusa da gidajensu.”

Kafin ta gama karatunta a jami’a, San Dan Ci Ji tana zaton cewa, watakila za ta ci gaba da zamanta a manyan birane, kamar birnin Shanghai da sauransu. Amma, a karshe, ta koma birnin Lhasa, ta fara aiki a cibiyar al’adun Tihho, wata hukuma dake yada da goyon bayan al’adun yankin Tibet, domin ta rika ba da gudummawarta wajen raya al’adun garinta. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)