Amurka ta sabawa ilmomin kimiyya yayin binciken asalin COVID-19
2021-08-19 18:53:25 CRI
A kwanakin baya, wani mai ido kan aikin binciken asalin COVID-19 na Amurka, ya fayyace cewa, ba a samu ci gaba ko kadan a binciken da hukumar leken asirin Amurka take gudanarwa ba, amma wasu manyan jami’an Amurka dai na ganin ya dace a yi bincike kan asalin wannan annoba, duk da ba hakan ne manufar kasar ba, kasancewar babbar manufar ta shi ne yiwa kasar Sin matsin lamba.
Tun bayan barkewar annobar, wasu ‘yan siyasar Amurka suna ta baza bayanan jabu domin bata sunan kasar Sin, matakan da suka dauka wajen gano asalin kwayar cutar sun sabawa ilmomin kimiyya, har sun kai ga illata hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa, yayin da suke kokarin kandagarkin annobar.
A karkashin matsin lambar Amurka, shirin gano asalin COVID-19 na mataki na biyu, da sakatariyar hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO ta gabatar wa kasashe mambobinta, domin su tattauna ya rasa tushen kimiyya da ruhin hadin gwiwa, a maimakon haka, an siyasantar da batun a cikin shirin.
Hakika a kwanakin baya, kasashe sama da 70 sun nuna goyon bayansu ga sakamakon da aka samu, yayin binciken asalin cutar bisa mataki na farko, ta hanyar aikawa babban jami’in hukumar WHO sakwanni, ko gabatar da sanarwa, ko takardun diplomasiyya, inda suka nuna adawa da siyasantar da batun gano asalin cutar.
Kana rahoton jin ra’ayin jama’a da kungiyar masanan CGTN, wato gidan talibijin na kasa da kasa na kasar Sin, wanda ke karkashin jagorancin CMG ta fitar shi ma ya nuna cewa, masu amfani da kafar intanet wadanda suka kada kuri’a kaso 80 bisa dari suna ganin cewa, an riga an siyasantar da batun gano asalin cutar, kuma kaso 83.1 bisa dari suna goyon bayan hukumar WHO, ta gudanar da bimcike kan kasar Amurka domin gano asalin COVID-19. A bayyane hakan ya tabbatar da cewa, wannan shi ne rokon al’ummun kasa da kasa. (Jamila)