Illar bayanan jabu tana komawa kan Amurka
2021-08-18 18:52:52 CRI
Tsohon shugaban kasar Amurka ya kan yi tsokaci da cewa, labaran jabu ne, yanzu haka labaran jabu suna bazuwa a fadin kasar, musamman ma tun bayan barkewar annobar cutar numfashi ta COVID-19, bayanan jabu da aka gabatar game da annobar suna karuwa bisa babban mataki, har sun boye ilmomin kimiyya, da tunanin basira da ake bukata yayin kandagarkin yaduwar annobar.
A farkon barkewar annobar, gwamnatin kasar Amurka ta kasa kula da gargadin da aka yi mata, ta rasa dama mai muhimmanci ta hana yaduwar cutar, kuma abin bakin ciki shi ne, ‘yan siyasar Amurka suna yayata bayanan jabu domin kare moriyarsu. A sa’i daya kuma, hankalin al’ummun kasar ya tashi sakamakon shan wahalar yaduwar annobar, ban da haka, manyan kafofin watsa labaran kasashen yamma ba su karyata bayanan jabu ba, bisa fakewa da ‘yancin bayyana ra’ayi.
Misali siyasantar da kwayar cutar, da bata sunan kasar Sin wai kwayar cutar ta fito ne daga dakin gwajin kasar, duk da cewa, shugaban kasar Amurka ya sauya, amma matakin da suka dauka bai canja ba, kullum suna dora laifi ga kasar Sin.
A halin da ake ciki yanzu, adadin Amurkawa wadanda aka tabbatar da cewa sun kamu da cutar COVID-19 ya riga ya kai miliyan 37, kuma gaba daya adadin mutanen da suka rasu sakamakon harbuwa da cutar ya kai dubu 620, adadin da shi ne mafi yawa a fadin duniya. Hakikanin abubuwan da suka faru sun nuna cewa, Amurka ta gaza dakile annobar daga duk fannoni, yayin da illar bayanan jabu da take yadawa ke komawa kanta. (Jamila)