logo

HAUSA

An samu raguwar hauhawar farashin kayayyaki cikin watan Yuli a Nijeriya

2021-08-18 10:22:47 CRI

An samu raguwar hauhawar farashin kayayyaki cikin watan Yuli a Nijeriya_fororder_32fa828ba61ea8d3f3363b9206bca949241f5849

Hukumar kididdiga ta Nijeriya NBS, ta ce alkaluman hauhawar farashin kayayyaki a kasar ya dan ragu zuwa kaso 17.38% a watan Yuli daga kaso 17.75% da ya kasance a watan Yunin. Tun daga watan Afrilu ake samun raguwar alkaluman, wato watanni 4 ke nan a jere.

Farashin kayayyakin abinci kuwa, ya karu zuwa kaso 21.03 a watan na Yuli idan aka kwatanta da kaso 21.83 da ya kasance a watan Yuni, lamarin dake nuna cewa farashin kayayyakin abinci ya ci gaba da hawa a watan Yuli, sai dai saurinsa bai kai na watan Yuni ba.

Hukumar ta bayyana cewa, an samu karuwar alkaluman farashin abinci ne sanadiyyar karuwar farashin madara da kofi da ganyen shayi da cocoa da chukwi da kwai da kayayyakin lambu da burodi da nama da sauran wasu abubuwan sha. (Fa’iza Mustapha)