logo

HAUSA

Na’urar binciken duniyar Mars ta Zhurong ta gama aikin binciken da aka tsara

2021-08-18 14:17:13 CRI

Na’urar binciken duniyar Mars ta Zhurong ta gama aikin binciken da aka tsara_fororder_zhurong-1

Rahotanni daga hukumar binciken sararin samaniya ta kasar Sin na nuna cewa, ya zuwa ranar 15 ga wannan wata, na’urar binciken duniyar Mars ta Zhurong, ta gudanar da aiki har na tsawon kwanaki 90 bisa ma’aunin duniyar Mars, wato kwanaki 92 bisa duniyarmu, inda ta yi tafiyar mita 889, da yin bincike da tattara alkaluman kididdiga da suka kai GB 10, wannan na nuna cewa, na’urar Zhurong ta gama aikin binciken da aka tsara cikin nasara. A halin yanzu, na’urar na gudanar da aikinta yadda ya kamata, da isasshen makamashin da take da shi, kuma za ta ci gaba da yin aiki a zirin dake iyakar teku da kasa dake kudancin yankin Utopia Planitia.

A ranar 23 ga watan Yuli na shekarar bara, aka harba kumbon binciken duniyar Mars na Tianwen-1 zuwa sararin samaniya cikin nasara, bayan da ya yi tafiya har na tsawon kwanaki 202, kimanin kilomita miliyan 475, ya shiga falakin dake kewayen duniyar Mars a watan Febrairu na bana. A ranar 15 ga watan Mayu, kumbon Tianwen-1 ya sauka a kudancin yankin Utopia Planitia cikin nasara. Bayan kwanaki 7, na’urar binciken duniyar Mars ta Zhurong, ta fara tafiya a kan duniyar Mars tare da yin bincike, inda ta dauka hotuna da dama game da wurin da kumbon ya sauka, da kasar dake duniyar Mars da sauransu.

A yayin da na’urar take gudanar da aikin bincike, na’urar ta gudanar da aiki kamar yadda aka tsara na kwanaki bakwai bakwai, da tsara shirin yin aikin bincike a kowace rana. Babban darektan kula da tsarin tafiya na kumbon Tianwen-1, Mr.Liu Jianjun ya yi bayani cewa, ya zuwa yanzu, an riga an samu bayanan dake shafar yanayin kasa, da sinadaran da ke kan duniyar, da karfin maganadisu da sauransu. Ya ce, “Game da tudun rairayi dake kan duniyar Mars kuwa, a halin yanzu, mun ga tudun rairayi masu siffar duniyar wata. Kana bisa hotunan da muka dauka, akwai bambanci a tsakanin tudun rairayi da muka kalla da tudun rairayi da sauran kasashe suka gano. Sai mun yi bincike kan su, kafin mu gano yanayin duniyar Mars, ko akwai canjin yanayin duniyar a baya? Za mu ci gaba da yin bincike kan yanayin kasa da sinadarai, don samun karin haske dangane da muhallin duniyar Mars a yanzu da ma a baya.”

Ya zuwa yanzu, na’urar binciken duniyar Mars ta Zhurong, ta gudanar da aiki a duniyar Mars har na tsawon kwanaki 90 bisa ma’aunin duniyar, ba da jimawa ba tsawon tafiyarta zai zarce mita 900. Abin dake jan hankalin al’umma shi ne, za a samu katsewar sadarwar na’urorin bincike a sakamakon yadda duniyar rana za ta tafi a tsakanin duniyar Mars da ta duniyarmu nan da wata guda, wanda zai sa ba a za a iya tuntubar kumbon Tianwen-1 har na tsawon kwanaki kimanin 50 ba. A lokacin, na’urorin binciken za su dakatar da aikin bincike. Babban mai zana tsarin binciken duniyar Mars na Tianwen-1 Sun Zezhou ya bayyana cewa, “A lokacin, ba za mu iya tuntubar kumbon Tianwen-1 yadda ya kamata. Don haka, na’urar binciken duniyar Mars, za ta yi aiki da kanta na tsawon wata fiye da daya, kamar kiyaye tsaronta, da bincike da warware matsalolinta da sauransu.”

Game da wannan kalubalen da za a fuskanta, babban darektan cibiyar kula da zirga-zirgar sararin samaniya ta kasar Sin Cui Xiaofeng ya bayyana cewa, sun riga sun shirya sosai. Ya ce, “A wannan karo, rana za ta jima da tafiya a tsakanin duniyarmu da duniyar Mars, don haka ya kamata a tsara shiri da zai kyautata aikin na’urorin binciken duniyar Mars, da tsara dukkan shirye-shirye kafin lokaci. Kana za mu kara sa ido kan na’urorin, bayan karewar lokacin, idan an gamu da wani yanayi maras kyau ba zato ba tsamani, to, ya kamata a daidaita shi yadda ya kamata.” (Zainab)