logo

HAUSA

’Yan bindiga sun kashe mutane 7 a Najeriya

2021-08-18 09:38:16 CRI

Rahotanni daga Najeriya na cewa, dan sanda daya da wasu fararen hula guda 6 sun gamu da ajalinsu, a wani hari da ’yan bindiga suka kai ranar Litinin din da ta gabata, wurin da ake aikin gina tashar samar da mai da iskar gas a jihar Imo dake yankin kudancin kasar.

Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar Micheal Abattam, ya bayyana cewa, mamatan na kan hanyarsu ce ta zuwa wurin da ake aikin gina tashar, lokacin da ’yan bindigar suka yi musu kwantom bauna a Assa, dake yankin karamar hukumar Ohaji-Egbema.

Abbatam, ya fadawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua ta wayar tarho cewa, har yanzu ba a san dalilin kai wannan harin ba. Sai dai rundunar ’yan sandan ta ce, ta dauki dukkan matakan da suka dace na kare rayukan ma’aikatan dake yankin, mai fama da hare-hare.

Jami’in ya kara da cewa, ’yan bindigar sun arce, bayan aikata wannan danyen aiki kan ma’aikatan dake aikin gina tashar, amma ’yan sanda sun kaddamar da bincike don gano maharan. (Ibrahim Yaya)