logo

HAUSA

Kasar Sin Daya Ce Tak A Duniya

2021-08-18 17:06:07 CRI

Kasar Sin Daya Ce Tak A Duniya_fororder_微信图片_20210818164117

Daga IbrahimYaya

Kasashe suna kulla huldar diflomasiya da kasar Sin, bisa sharadin martaba manufar nan ta kasar Sin daya tak a duniya. Sai dai a wasu lokuta irin wadannan kasashe na keta wannan yarjejeniya, ko dai bisa kuskure ko ganganci ko kuma ingiza mai kanto ruwa, don kawai su faranta ran iyayen gidansu.

Kasar Lithuania na daga cikin kasashen da suka kulla huldar diflomasiya da kasar Sin, bisa amincewa da ma mutunta manufar kasar Sin daya tak a duniya. Amma sai aka wayi gari kasar Lithuania ta karya wannan sharadi, inda amincewa mahukuntan yankin Taiwan na kasar Sin, su bude ofishin wakilci da sunan Taiwan, sanin kowa ne cewa, wannan mataki ya saba manufar kasar Sin daya tak a duniya, abin da ya sa, kasar Sin yanke shawarar kiran jakadanta dake kasar Lithuania, tare da umartar ita ma Lithuania, da ta janye nata Jakadar dake kasar Sin. Yankin

Taiwan wani bangare ne na kasar Sin, wanda ba za a iya zaba shi ba.

Matakin da kasar Sin ta dauka, abu da ya dace, kuma duk wata kasa mai ’yanci, wajibi ne ta kare muradu da cikakkun yankunanta daga dukkan fannoni. Sai dai wani abin bakin ciki shi ne, bayan daukar wannan halartaccen mataki da kasar Sin ta yi, wasu kasashe da daidaikun mutane, suka fara yaudarar jama’a.

Masu fashin baki na cewa, duk kasar da take son kulla huldar diflomasiya da kawo ce kasa, wajibi ne su martaba ka’idoji da manufar diflomasiyar juna. Wannan ne ma ya sa, bangaren kasar Sin, ya nuna adawa da babbar murya kan zargin da Amurka ke yiwa matakin na kasar Sin, ta kuma bukaci kungiyar Tarayyar Turai (EU), da ta daina aikewa da mummunan sako kan batun da ya shafi moriyar kasar Sin ko haddasa wata sabuwar matsala a alakar Sin da EU.

Kasar Sin daya ce tak a duniya, kuma duk kasar dake son kulla alaka da ita, to, wajibi ne ta martaba wannan manufa. (IbrahimYaya)