Matsayar Kasar Sin Dangane Da Afghanistan Abar Dubawa Ce
2021-08-17 19:37:21 CRI
BY CRI HAUSA
A halin da ake ciki, dukkan hankalin duniya ya karkata zuwa yanayin da kasar Afghanistan ke ciki, biyo bayan kwace iko da ragamar kasar da kungiyar Taliban ta yi da kuma tserewar da shugaban kasar ya yi. Hankula sun tashi kuma bangarori daban-daban har ma da daidaikun mutane a fadin duniya, na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu dangane da abun da ya zo a ba-zata.
Dangane da halin da ake ciki ne mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar, Wang Yi ya tattauna da takwaransa na Amurka Anthony Blinken ta wayar tarho, bisa gayyatar bangaren Amurka. A cewar Wang Yi, abubuwan da suka auku a Afghanistan, sun shaida cewa, bai kamata a tilastawa wata kasa tsarin da ba nata ba, domin kasa da kasa sun bambanta ta hanyar tarihi da al’adu da sauransu. Wannan wani abu ne da kullum kasar Sin ke nanatawa kasashen yammacin duniya. Kamar yadda kowane mutum a duniya ya bambanta da wani, haka kasashen duniya ma suka sha bamban. Duk da cewa harkokin rayuwa da makoma ko burika na da alaka da juna, dole ne a samu bambancin ra’ayi da al’adu. Abun da ya yi wa wata kasa kyau, ba lallai ne ya dace da wata kasa ba. Wannan kadai ya isa ya zama darasi ga Amurka da ta shafe shekaru 20 a Afghanistan da sunan yaki da Taliban. Duk da dimbin kudaden da ta kashe da sojojin da ta yi asara cikin wadancan shekaru, cikin kankanin lokaci sun bi ruwa domin dai ga shi yanzu Taliban din ta kwace iko da Afghanistan, wani abu da ke nuna cewa Amurka, ba ta ko kama hanyar karya lagon kungiyar ba. A matsayinta na kasa mai cikakkakken ’yanci, ya kamata kasa da kasa su girmama wannan da kuma zabin da al’ummar kasa suka yi. Danniya da fin karfi da kuma babakere, ba za su taba haifar da da mai ido ba, sai ma dai dimbin asarar dukiya da rayuka.
Wang Yi ya kara da cewa, Sin na fatan tattaunawa da Amurka da zummar tabbatar da zaman lafiya a kasar Afghanistan. Hakika abu mafi dacewa a yanzu shi ne, kokarin wanzar da zaman lafiya a kasar domin kaucewa rikice-rikice da karuwar ayyukan ’yan ta’addanci. Maimakon kara ta’azzara yanayi ko tura sojoji domin shiga yaki, ya kamata a yi nazarin halin da kasar ke ciki don bada taimakon da ya dace da ita. Al’ummar Afghanistan sun shiga mawuyacin hali cikin gomman shekarun da aka shafe ana yaki a kasar, don haka, ya kamata a sauya dabara, su ma kamar kowa, sun cancanci samun zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma ci gaba. (Fa’iza Mustapha)