logo

HAUSA

Hima Oumarou Souleymane: Jagorancin JKS da kishin kasa da aiki tukuru su ne sirrin ci gaban kasar Sin

2021-08-17 13:09:13 CRI

Hima Oumarou Souleymane: Jagorancin JKS da kishin kasa da aiki tukuru su ne sirrin ci gaban kasar Sin_fororder_AA

Hima Oumarou Souleymane, wani dan Nijar ne wanda ya yi shekaru 10 yana karatu da zama a kasar Sin, musamman a lardin Hebei dake arewacin kasar. Yanzu malam Hima yana neman digiri na uku a fannin watsa labarai da aikin jarida a jami’ar Hebei.

Hima Oumarou Souleymane: Jagorancin JKS da kishin kasa da aiki tukuru su ne sirrin ci gaban kasar Sin_fororder_BB

Hima, wanda ke sha’awar al’adun gargajiya da tarihin kasar Sin sosai, ya taba ziyartar wuraren tarihi da dama da suka shafi gwagwarmayar da jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ta yi don gina kasa, da halartar wasu muhimman taruka game da tarihin jam’iyyar na tsawon shekaru dari, inda ya bayyana ra’ayinsa cewa, jagoranci nagari na jam’iyyar, da yadda al’ummar kasar suke kishin kasa, da kuma jajircewarsu wajen aiki, duk sun sa kasar Sin ta samu ci gaba a fannoni daban-daban.

Har wa yau, a matsayin mutumin dake sha’awar wasan Kung-fu na kasar Sin, malam Hima yana da burin kara tallata wasan a gida Jamhuriyar Nijar, da bada gudummawarsa ga inganta musayar al’adun gargajiya tsakanin kasar Sin da Nijar da ma sauran kasashen Afirka. (Murtala Zhang)