logo

HAUSA

Amurka tana keta hakkin bil adama a fadin duniya

2021-08-17 19:01:03 CRI

Amurka tana keta hakkin bil adama a fadin duniya_fororder_amurka

Amurka ta kan kira kanta “mai kare hakkin bil adama”, ko da yake tana sabawa hakan, tare da tsoma baki a cikin harkokin gidan sauran kasashen duniya bisa fakewa da hakkin bil adama, amma yaduwar annobar cutar numfashi ta COVID-19 a kasar ta kara nunawa al’ummun kasa da kasa cewa, Amurka tana cikin yanayin rudani da tangarda da kuma rikici.

A cikin shekara daya da ta gabata, laifuffukan nuna karfin tuwo a kasar Amurka suna karuwa, kuma alkaluman da aka fitar sun nuna cewa, adadin laifuffuka da bindiga a kasar a shekarar 2020 ya kai 614, a sanadin haka mutane 521 sun rasa rayukan su. Kuma a farkon watanni bakwai na bana, adadin laifuffukan ya riga ya kai 410, inda mutane 437 suka rasu.

Yanzu haka kason aikata laifuffuka na Amurka ya kai sahun gaba a cikin kasashe masu ci gaba, ya kuma fi na wasu kasashe masu tasowa yawa, inda a cikin adadin, aikata laifuffuka bisa dalilin kin jinin saura ya fi bai wa al’ummun kasa da kasa mamaki. Misali wani mutum ‘dan asalin Afirka, George Floyd ya mutu a sanadin kisan gillar da wasu ‘yan sanda farar fata a jihar Minnesota ta kasar Amurka suka yi masa a watan Mayun bara, lamarin da ya nuna cewa, tsirarun al’ummun kasar suna gamuwa da nuna karfin tuwo, da raini da rashin adalci a cikin dogon lokaci.

Kana wani rahoto mai taken “mawuyacin halin da al’ummun Amurka ke ciki bayan barkewar annobar COVID-19”, wanda cibiyar kasafin kudi da manufofin fifiko ta Amurka ta fitar ya nuna cewa, a cikin watanni shida na farkon bana, al’ummun kasar da yawansu ya kai miliyan 20 suna fama da karancin abinci, kuma al’ummun kasar wajen miliyan 11 da dubu 400 ba su iya biyan kudin hayar gidajen kwana a kan lokaci, ta yadda mai yiwuwa a kore su daga gidajen kwanan a ko da yaushe.

Amma ‘yan siyasar Amurka sun yi watsi da matsalolin da al’ummun kasarsu ke fama da su, suna ta gurgunta yanayin kwanciyar hankali a sauran kasashen duniya. Hakikanin abubuwa dake faruwa sun shaida cewa, Amurka tana keta hakkin bil adama a fadin duniya. (Jamila)