logo

HAUSA

Najeriya: Kwalara ta hallaka mutane 1,178

2021-08-17 19:57:02 CRI

Cutar amai da gudawa ko cholera ta hallaka mutane 1,178 a jihohi 23, da birnin Abuja, fadar mulkin Najeriya, tun barkewar cutar a watan Janairun farkon shekarar nan.

Wasu alkaluma da cibiyar yaki da cututtuka ta Najeriya NCDC ta fitar, sun nuna cewa, ya zuwa ranar Asabar din karshen makon jiya, akwai mutane 37,819 da aka gabatar da rahoton yiwuwar kamuwar su da cutar.  (Saminu)