logo

HAUSA

Nijeriya ta fara zagaye na biyu na allurar riga kafin COVID-19

2021-08-17 14:57:29 CRI

Nijeriya ta fara zagaye na biyu na allurar riga kafin COVID-19_fororder_210817-faeza 5-Nigeria

An shiga zagaye na biyu na yi wa jama’a allurar riga kafin COVID-19 a Nijeriya, a jiya Litinin.

Sakataren gwamnatin Nijeriya Boss Mustapha, ya bayyana yayin kaddamar da shirin cewa, sama da allurai miliyan 4 na kamfanin Moderna da Amurka ta bada gudunmuwarsu ta hannun shirin COVAX ne za a yi amfani da su a wannan karo.

Gwamnatin Nijeriya na da burin yi wa kaso 40 cikin dari na al’ummarta riga kafin zuwa karshen bana, yayin da zuwa karshen 2022 kuma, take fatan adadin wadanda aka yi wa allurar ya kai kaso 70 cikin dari.

Nijeriya ta karbi kashin farko na alluran riga kafin COVID-19 kusan miliyan 4 ta hannun COVAX ne a farkon watan Maris, kana ta karbi allurai miliyan 4 na kamfanin Moderna a ranar 2 ga watan nan na Augusta. (Fa’iza Mustapha)