Kasar Amurka ta bayar da kudinta mafi yawa a duniya don mika rikicinta ga sauran kasashen duniya
2021-08-16 16:33:22 CRI
Dandalin kwararru 3 na kasar Sin sun fitar da rahoton nazari cikin hadin gwiwa game da hakikanin yanayin yaki da cutar COVID-19 da kasar Amurka ke ciki, inda aka yi nuni da cewa, game da gazawa kan matakan magance yaduwar cutar COVID-19 da gwamnatin kasar Amurka ta gudanar, baitulmalin kasar Amurka ya dogora ne kan aikin bayar da kudin Amurka mafi yawa don sassauta rikicin kasar. Amurka ta kara shigar da kudi zuwa kasuwanci, hakan zai kawo illa ga kasuwancin duniya da kuma jama’ar dukkan duniya baki daya.
A wasu shekarun da suka gabata, baitulmalin kasar Amurka ya dauki matakan kara bayar da kudi mafi yawa. Gwamnatin kasar Amurka da majalissun dokokin kasar sun zartas da wasu dokokin bada taimako don kara bayar da kudin Amurka fiye da triliyoyin dala. A halin yanzu, kasar Amurka tana mika yanayin hauhawar farashi ga sauran kasashen duniya. A sakamakon kudin Amurka kudi mai muhimmanci ne da aka ajiye a duniya, kara shigar da kudin Amurka a sauran kasashen duniya zai haddasa rashin tabbaci a kasuwar hannayen jari ta kasa da kasa.
Don tinkarar hadarin kara bayar da kudin Amurka, sabbin kasashe mafi samun ci gaba da kasashe masu tasowa sun dauki matakai, kamar Brazil, da Rasha, da Turkiya, da Mexico bi da bi ne sun daga farashin kudin ruwa a bankuna, hakan mai yiwuwa ne zai hana farfadowar tattalin arzikinsu.
A halin yanzu, jama’ar kasa da kasa suna fuskantar yanayin tinkarar cutar COVID-19, amma kasar Amurka ta bayar da kudinta mafi yawa sai dai an kawo matsin lamba ga sauran kasashen duniya a fannonin tattalin arziki da zamantakewar al’umma, kana hakan zai kawo hadari ga tsaron bunkasuwar tattalin arzikin duniya. (Zainab)