logo

HAUSA

Hou Xiuzhen: Kokarin raya ruhin Nanniwan na dogaro da kai da aiki tukuru

2021-08-16 21:19:27 CRI

Hou Xiuzhen: Kokarin raya ruhin Nanniwan na dogaro da kai da aiki tukuru_fororder_nanniwan1

Hou Xiuzhen wata mace ce da ta manyanta, wadda ke zaune a Nanniwan, wani kauye a gundumar Baota na Yan’an dake lardin Shaanxi na arewa maso yammacin kasar Sin. Hou da iyalinta na ajiye da hotunan tarihi na gangamin raya Nanniwan da ya fara a shekarun 1940. Hou ta kan bada labarin Nanniwan ga bakin da suka ziyarci gidanta. Ruhin gangamin raya Nanniwan kamar wuta ce mai ci da zuri’a 3 ta Hou suka gada.

Wata fitacciyar waka ce mai taken Nanniwan ta bayyana gagarumin sauye-sauyen da suka faru a Nanniwan tun bayan da aka kaddamar da gangamin a shekarar 1940.

Bisa labaran da ta ji daga surikinta, Hou Xiuzhen ta gaya mana cewa, “a cewar surikina, Liu Baozhai, a lokacin da aka tura sojojin kasar Sin su farfado da yankunan da aka yi watsi da su da raya ayyukan gona, su kan tsinci tsirran daji su dafa su ci. Sun sare bishiyoyi da tattara ciyayi domin samar da matsugunin. Su kan shirya gasa domin kara inganta bude yankunan,”

An haifi Liu Baozhai ne a shekarar 1897 a Shenqiu, wata gunduma a lardin Henan dake yankin tsakiyar kasar Sin. Ya kuma shiga masu juyin juya hali ne a lokacin da yake shekara 16, daga baya kuma ya samu shiga rundunar sojin kasar Sin na wancan lokaci. Ya taba zama mataimakin kwamanda a runduna mai lamba 359. Rundunar da aka tura Nanniwan domin shiga gagarumin gangamin. Shekaru 3 bayan nan, zaratan sojojin suka mayar da yankunan da aka yi watsi da su zuwa na noma, inda ake kiwon raguna da shanu, haka kuma aka kafa kananan masana’antu.

An haifi Hou Xiuzhen ne a Henan a 1946. A lokacin da take matashiya, ta je Nanniwan da iyayenta. Kamar iyayen Hou, gomman iyalai daga Henan ne suka kaura zuwa Nanniwan domin aiki da mutane kamar Liu Baozhai wadanda suka fito daga garin su ma. “Duk da ban taba shiga wani gangamin ba, na samu labarai game da sojojin Nanniwan a lokacin da nake yarinya. An karfafa min gwiwar daukar darasi daga sojojin”, cewar Hou. Sannu a hankali, ruhin dogaro da kai da aiki tukuru ya samu wajen zama a zuciyarta.

Bayan kafuwar Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin a 1949, sai Liu Baozhai ya zabi zama a Nanniwan domin ci gaba da kare yankin. Ya kan ba baki labaran wajen. Ya yi imanin cewa, bayar da labarin juyin juya hali abu ne mai muhimmanci. Liu ya mutu a 1984. Don haka Hou ta yanke shawarar ci gaba da jajircewa wajen bayar da labarin Nanniwan.

Hou Xiuzhen tana ajiye wani daga cikin kayayyakin aikin surikinta, wanda yake noma da shi yayin gangamin. Tana girmama shi saboda ya kasance abu mai daraja ga iyalinta, wanda ke tunatar da ita ruhin dogaro da kai da aiki tukuru. Hou ta fahimci akwai hakkin da ya rataya a wuyanta, wanda ta gada daga magabata sa’annin surikinta.

“Dole ne in kasance mai hidimtawa jama’a da daukar matakai a aikace domin inganta rayuwarsu. Ta wannan hanya ce kadai zan iya ci gaba da cika burin da na gada daga surikina,” cewar Hou.

Ta rike mukamai da yawa a kauyen, ciki har da shugabar kwamitin kauyen Nanniwan da sakatariyar reshen JKS dake kauyen.

Hou Xiuzhen: Kokarin raya ruhin Nanniwan na dogaro da kai da aiki tukuru_fororder_nanniwan2

Daga shimfida hanya, kafa makaranta, da jagorantar mutanen kauyen samun kudin shiga zuwa yin sulhu a tsakanin mazauna, Hou ta dauki batutuwan da suka shafi kauyen tamkar na iyalinta. Ta kan hidimtawa mutanen kauyen da zuciya daya, tamkar na ‘yan uwanta. Sadaukarwarta ga Nanniwan ya kai ta ga samun aminci da yabo daga mazauna wurin.

A baya, babu makarantar firamare a Nanniwan. Sai yara sun tsallake kogi tare da yin tafiya zuwa kauyen Yangwan dake makwabtaka da su, domin zuwa makaranta. Domin warware wannan matsala, Hou Xiuzhen ta yi kira ga mazauna kauyen don a gina makaranta. Sun shafe sama da wata 1 suna aiki ba dare ba rana. A shekarar 1979, Nanniwan ya samu makarantar firamare ta farko.

A 1999, Hou da sauran jama’a da mambobin JKS, suka amsa kiran gwamnatin kasa na shuka bishiyoyi da inganta muhallin hallitu. “Tun da kasarmu ta yi kira da mu mayar da gonaki zuwa dazuka, dole ne mu shuka bishiyoyi da tabbatar da muhallin kauyenmu bai lalace ba,” cewar Hou. 

Hou da sauran mutanen kauyen sun shafe shekaru suna shuka bishiyoyi a kan tsaunika. “har yanzu na kan tuna gungun bishiyoyin da muka fara shukawa shi ne bishiyoyin Pagoda. Suna girma da wuri kuma wasu sabbi na ci gaba da tsirowa. Mutane da dama kan tambaye ni, ‘Hou, jimilar bishiyoyi nawa kika shuka?’ Ba na iya fadar ainihin adadin, na shuka bishiyoyi a kan kwari da tsaunika da dama.” A cewar Hou, bishiyoyin da yanzu ke girma a kan tsaunika suna hana ambaliyar ruwa. Mutanen kauyen sun samu tallafin kudi saboda sun mayar da gonaki zuwa dazuka. Suna samun karin kudin shiga domin tallafawa ‘ya’yansu, ta yadda za su samu ingantaccen ilimi. Wasu daga cikin yaran sun shiga jami’o’i yayin da tuni wasu suka kammala, har ma wasu sun mallaki shaidar digirin digirgir.

Yanzu Nanniwan na da tsaunikan dake lullube da bishiyoyi da tsirrai, haka kuma kasansu na kewaye da furanni masu kyau da fadamu da gonakin shinkafa. Namun daji da ba kasafai ake ganinsu ba, sun sake bayyana a kan tsaunika da kuma cikin dazukan, sannan muhalli ya samu ingantuwa sosai. Hou ta ce, “a baya, mun farfado da yankunan domin raya aikin gona, ta yadda za mu samu karin abincin da za mu ci. Yanzu kuma, muna shuka bishiyoyi domin kyautata rayuwarmu. Mambobin JKS da suke sa’annina da sa’annin surikina, mun nace ga burikanmu, kuma mun cika alkawarinmu a matakan tarihi daban-daban.”

Hou Xiuzhen: Kokarin raya ruhin Nanniwan na dogaro da kai da aiki tukuru_fororder_南泥湾3

Tun bayan mutuwar Liu Baozhai, Hou Xiuzhen ke bayar da labaran Nanniwan ga baki. “Ba cikin sauki muka samu rayuwar da muke yi yanzu ba. Sai da magabatanmu suka yi sadaukarwa mai yawa, ciki har da rayukansu domin tabbatar da ‘ya’yansu, mu, mun samu rayuwa mai kyau. Dole mu rika tunawa da su,” a kan jiyo ta tana bada labarin ga baki. “ A matsayin mazauniyar Nanniwan, kuma surikar tsohon sojan da ya hidimtawa rundunar sojin kasar Sin, ina alfahari sosai. Babban tasirin da surikina ya yi kai na shi ne ruhin Nanniwan, wanda ke bukatar mu dogara da kanmu da yin aiki tukuru.”

Bayan Hou Xiuzhen ta yi ritaya a 2001, ‘yarta Zhang Fengqin, ta ba ta shawarar komawa birni domin more rayuwa. Sai dai, Hou ta dage za ta zauna a kauyen, saboda ta yi imanin tana da muhimmin aiki. Hou ta ce, “da yawa daga cikin ‘ya’yan sojojin runduna mai lamba 359 sun mutu. Idan ban zauna na ba baki tarihin mutanen da suka yi aiki tukuru a nan ba, wa zai ci gaba da daukaka ruhi da tarihin Nanniwan? Idan na yi tsufan da ba zan iya bayar da labarin ba, zan nemi ‘yata ko surikina ko jikana, su ci gaba da bayar da labaran.”

Cikin sama da shekaru 30 da suka gabata, Hou ta bayar da tarihin Nanniwan ga dalibai da manema labarai da masu yawon bude ido da ma’aikatan kamfanoni da hukumomin daban-daban. A duk lokacin da ta tuna baya, lokacin da sojoji ke aikin raya yankunan da aka yi watsi da su a Nanniwan, ta kan yi kuka. Jajircewar sojojin ga raya Nanniwan, kan taba zuciyar mutanen dake sauraron labaran. 

Hou ta kara da cewa, “bisa fahimtata, hidimtawa jama’a na nufin jure wahalhalu da farko da kuma more kyakkyawan sakamako, da warware matsaloli da kanmu da saukaka rayuwar sauran mutane.” Surikinta ne ya kan furuta wadannan kalamai lokacin da yake raye. Hou ta rubuta wadannan kalamai cikin wasikar da ta aike na neman zama ‘yar JKS. Ta kan fadawa matasa cewa, “yanzu, muna rayuwa ne a sabon zamani. Amma, kada mu manta cewa, abun da muke da shi yanzu, sakamako ne daga magabatanmu, wadanda suka yi aiki tukuru karkashin jam’iyyarmu. Ya kamata mu gaji ruhin hidimtawa jama’a, da koyi da magabata domin aiki tukuru, ta yadda kasarmu za ta kara karfi.”

Da taimakon ‘ya’yanta da jikoki, Hou Xiuzhen ta kafa dakin nune-nune, inda aka bayyana hotuna da tarihin katafaren gangamin raya Nanniwan. Ta yi imanin cewa, bada labarin ruhin Nanniwan da na kauyen, ita ce kyauta mafi dacewa da iyalinta za ta ba JKS yayin cikarta shekaru 100 da kafuwa.

Kande