logo

HAUSA

Tsarin siyasar Amurka ba zai bar ta ta kawo karshen yaduwar COVID-19 ba

2021-08-15 20:18:46 CRI

Tsarin siyasar Amurka ba zai bar ta ta kawo karshen yaduwar COVID-19 ba_fororder_amurka

An lura cewa, likitocin kasar Amurka suna iya warkar da wadanda suka harbu da cutar COVID-19, duba da cewa, tsohon shugaban kasar ya warke daga cutar cikin sauri, kuma ya koma gida daga asibiti a kan lokaci, amma cikin mutane miliyan 36 da suka harbu da cutar a cikin kasar, fiye da dubu 600 sun rasa rayuka, halin da al’ummun Amurka suka tsinci kansu, ta sha bamban matuka, lamarin da ya sake shaida cewa, tsarin siyasar kasar dake haddasa rarrabuwar kawuna, yana kawo tarnaki ga daukacin manufofin dake shafar moriyar jama’a a kasar.

A kasar ta Amurka, gwagwarmayya dake tsakanin jam’iyyar Democrat da ta Republican tana kawo sabanin siyasa a fadin kasar, ‘yan siyasar kasar sun saba da daukar matakai bisa la’akari da moriyar siyasa, yayin da suke fuskantar yaduwar annobar cutar numfashi ta COVID-19, a ganinsu, ikon siyasa ya fi kome muhimmanci, a don haka sun yi watsi da moriyar al’ummun kasar da kuma tsaron rayukansu, wannan ya sa Amurka, wadda ke sahun gaba a fadin duniya a fannonin fasahohin likitanci da kwararru da kayayyakin kiwon lafiya, ta gaza dakile yaduwar cutar, yanzu haka tarin al’ummun kasar suna shan mummunan wahala sakamakon yaduwar annobar.

A halin yanzu, jam’iyyun siyasa a Amurka suna ta yada labaran jabu da dama domin shaida tsarin siyasarsu, har sun yi watsi da bayanan kimiyya, tare da tayar da hargitsi da sabon cacar baki, duk wadannan ba ma kawai sun kawo illa ga yanayin kandagarkin annoba a cikin gida ba, har ma sun gurgunta hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa yayin da suke kokarin dakile yaduwar annobar.(Jamila)