logo

HAUSA

Sin za ta ci gaba da bude kofa ga waje domin samar da sabbin damammaki ga kasa da kasa

2021-08-13 14:31:40 CRI

Sin za ta ci gaba da bude kofa ga waje domin samar da sabbin damammaki ga kasa da kasa_fororder_hoto

Gabannin matsalar yaduwar cutar COVID-19 tsakanin kasa da kasa a shekarar 2021, tattalin arzikin kasar Sin ya fara samun farfadowa cikin yanayin karko. Yadda kasar Sin take kokarin tsara sabon shirin neman bunkasuwa, da kuma kara bude kofa ga waje, ya samar da sabbin damammaki masu kyau ga kasa da kasa.

Maryam Yang na dauke da karin bayani…

“Cikin farkon rabin shekarar bana, jimillar kayayyakin shige da fice na kasar Sin ta kai RMB yuan triliyan 18.07, adadin da ya kai matsayin koli cikin tarihin kasar Sin, wanda ya karu da kashi 22.8 bisa dari, idan aka kwatanta da makamancin lokaci na shekarar 2019. Kuma, jimillar kayayyakin shige da fice na Sin yana karuwa wata bayan wata, cikin watanni 13 da suka gabata.”

A tsakiyar shekarar bana, babbar hukumar kwastam ta kasar Sin ta fidda bayani dake cewa, ci gaba na karuwar cinikayyar kayayyakin shige da fice na kasar Sin, ya samar da damammaki masu kyau ga kasa da kasa.

A lokacin da kasar Sin take hadin gwiwa da kasashen duniya domin yaki da cutar COVID-19, bayan cutar ta barke tsakanin kasa da kasa, a sa’i daya kuma, kasar Sin tana ci gaba da bude kofa ga waje.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sha jaddada cewa, duk wanda ke neman bata dunkulewar kasa da kasa bisa hujjar dakile yaduwar annoba, zai bata moriyar kansa. Kasar Sin tana kokarin raya sabon tsarin neman bunkasuwa, ta hanyar karfafa karfin tattalin arziki da kuma kara bude kofa ga waje, ta yadda sauran kasashen duniya za su sami damammaki masu kyau bisa bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin.

A watan Janairu na bana, Xi Jinping ya sake jaddada matsayin kasar Sin na kara bude kofa ga waje, yayin taron tattaunawar tattalin arzikin duniya na Davos. Ya ce,“Kasar Sin tana goyon bayan dunkulewar kasa da kasa a fannin tattalin arziki, da kuma tsayawa tsayin daka kan manufar bude kofa ga waje. Za ta ci gaba da inganta ayyukan ciniki da zuba jari cikin ’yanci, da kuma kiyaye tsarin samar da kayayyaki na kasa da kasa, domin karfafa shawarar “Ziri daya da hanya daya” yadda ya kamata.”

A shekarar 2013, Xi Jinping ya fidda shawarar “Ziri daya da hanya daya” a karo na farko. Ya zuwa yanzu, ta riga ta kasance babban dandalin hadin gwiwar kasa da kasa. Kasashe 140 sun kulla yarjejeniyar hadin gwiwa da kasar Sin bisa wannan shawara, kuma, jimillar cinikin dake tsakanin kasar Sin da kasashe abokanta, ya zarce dalar Amurka triliyan 9.2, kana, adadin jarin da kamfanonin kasar Sin suka zuba cikin wadannan kasashe ya kai sama da dalar Amurka biliyan 130.

Bayanin bankin duniya ya nuna cewa, ya zuwa shekarar 2030, aikin gina shawarar “Ziri daya da hanya daya” cikin hadin gwiwa, zai ba da taimako ga mutane miliyan 7.6 cikin kasashen duniya wajen kawar da talauci mai tsanani, da kuma ba da taimako ga mutane miliyan 32 wajen kawar da talauci mai matsakacin matsayi. Shawarar “Ziri daya da hanya daya” za ta kasance babbar shawarar neman wadata ga dukkanin bil Adama.

Haka kuma, yayin dandalin tattaunawar kasashen Asiya na Boao na shekarar 2021, Xi Jinping ya sake gayyatar kasa da kasa, da su shiga aikin gina shawarar “Ziri daya da hanya daya” cikin hadin gwiwa. Yana mai cewa,“Bisa shawarar “Ziri daya da hanya daya”, kasashen duniya za su hada kansu domin neman bunkasuwa tare, a maimakon neman bunkasuwar wata kasa daya kadai. Dukkan kasashe dake da sha’awar wannan shawara za su iya halartar ta, domin yin hadin gwiwa, da kuma cimma moriyar juna. Muna neman bunkasuwa, da fatan cimma moriyar juna, da kuma samar da kyawawan damammaki bisa wannan shawara.”

Bude kofa ga waje, da cimma moriyar juna, sun dace da bukatar kasa da kasa, kuma su ne fatan kasar Sin. Kasar Sin za ta ci gaba da karfafa hadin gwiwar kasa da kasa domin raya tattalin arzikin duniya, bisa ka’idojin kara bude kofa ga waje, da nuna fahimtar juna, da samar da moriya ga kowa da kowa, da neman daidaito, da kuma cimma nasara cikin hadin gwiwa. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)