logo

HAUSA

Ren Jiaojiao, masaniyar kasar Sin da ke aikin binciken masara a "garin" masara

2021-08-13 10:07:11 cri

A matsayinta na muhimmiyar kasa a Latin Amurka, an kuma san kasar Mexico da “Garin masara”. A halin yanzu, Ren Jiaojiao, wata matashiya kuma masaniya a fannin aikin gona daga kasar Sin tana koyo da yin nazari kan aikin renon irran masara dake iya yaki da cututtuka ta hanyar gadon dabi’un halitta, a lokaci guda kuma, tana kokari don inganta sada zumunci da hadin gwiwa a fannin aikin gona tsakanin kasashen biyu.

An shigar da Ren Jiaojiao Jami'ar Aikin Gona ta Kasar Sin a shekarar 2006. A lokacin karatunta na samu digiri na farko, da na biyu da kuma digiri na uku, tana karatu a Cibiyar Inganta Masara ta Kasa ta Jami'ar Aikin Gona ta Kasar Sin, wadda ta kasance hukumar koli a fannin nazarin harkar masara a kasar. A shekarar 2017, Ren Jiaojiao, wadda ta sami digiri na uku, ta shiga Jami'ar Aikin Gona ta Xinjiang, don soma aikin nazarin dabi’un hallita na masara. A watan Oktoba na shekarar 2019, ta zo Cibiyar Inganta Masara da Alkama ta Duniya a jihar Meksiko dake tsakiyar Mexico don ci gaba da nazarinta kan renon irran masara masu yaki da cututtuka ta hanyar gadon dabi’un halittu.

Ren Jiaojiao, masaniyar kasar Sin da ke aikin binciken masara a "garin" masara_fororder_rjj

Dangane da zabar aikin gona a matsayin aikinta a duk tsaron rayuwarta, Ren Jiaojiao ta ce:

“Tun daga shekarar 2004, takardar Gwamnatin Tsakiya ta kasarmu mai lamba 1 ta ci gaba da mai da hankali kan batutuwan da suka shafi aikin gona da yankunan karkara da manoma. Ina tsammanin sadaukar da kaina ga ci gaban aikin gona zai taimaka wajen tabbatar da kwarewa ta. Tashi da faduwar aikin gona yana da alaka da makomar kasar, kuma aikin gona mai karfi abu ne mai mahimmanci wajen tabbatar da kwanciyar hankali da zaman karko ga wata kasa. Musamman tun shekarar da ta gabata, shugaban kasarmu Xi Jinping ya ba da shawarar "Yin gwagwarmaya mai kyau a fannin masana'antar irrai". Binciken da nake yi kan renon irran masara masu yaki da cututtuka ta hanyar gadon dabi’un halittu ya shafi wata muhimmiyar fasaha wajen ci gaban masana’antun iri na kasarmu. Don haka, ina tsammanin sana'ar da nake karantawa da kuma gudanarwa tana da makoma ta ci gaba mai kyau, kuma a shirye nake in ba da gudummawa ga wannan sana'ar.”

Ban da gudanar da aiki a dakin gwaje -gwaje, babban aikin masana a fannin kimiyyar aikin gona shi ne yin aiki a cikin gonaki a karkashin rana mai zafi. Ga matasa na zamani wadanda suka saba da kwandishan da WIFI, watakila abin da suke ji kan wannan sana’a shi ne "aiki mai wahala". Amma game da irin wannan "aiki mai wahala ", Ren Jiaojiao tana farin ciki sosai, ta ce,

“Tabbas muna aikin tukuru. Babban kalubale da wahala a gare mu wajen gudanar da wannan sana'ar, ita ce mun fi yin aiki a gonaki kuma a galibin lokaci muna fuskantar iska mai karfi ko kuma rana mai zafi. Amma don samun bayanan gwaji na gaske, lallai ya zama dole mu kammala yawancin ayyukanmu a gona, wanda kuma jarrabawa ce a gare mu.”

Ren Jiaojiao, masaniyar kasar Sin da ke aikin binciken masara a "garin" masara_fororder_rjj2

Babban binciken Ren Jiaojiao shi ne wane irin cuta duk duniya ke fuskanta wajen noman masara. Idan masara ta kamu da irin cutar, to ga yanayi mafi muni, zai iya haifar da raguwar kayan aikin har zuwa kashi 50%. Abun da take dora muhimmanci wajen nazarinsa, ba a gudanar da bincike sosai kansa ba a kasar Sin a cikin 'yan shekarun nan, amma Cibiyar Inganta Masara da Alkama ta Kasa da Kasa ta Mexico tana da fasaha mafi inganci a duniya a wannan fannin. Ana iya cewa, aikin nazari da Ren Jiaojiao da abokan aikinta suke gudanarwa, yana da kyakkyawar ma'ana ga aikin renon irran masara masu aki da cututtuka ta hanyar gadon dabi’un halittu na kasar Sin, da ta Mexico, har ma da na duniya baki daya.

Ren Jiaojiao ta ce, kasar Mexico ita ce asalin masara kuma tana da albarkatun irrai daban daban. Wasu yankuna a kudu maso yammacin kasar Sin suna da kamanceceniya a fannonin yanayin kasa da Mexico, don haka kasar Sin tana da dama mai kyau ta shigo da irrai da fasahar noman masara ta Mexico.

“Ina mayar da hankali kan nazarinmanyan manufofi a fannin, don haka dalilin zuwana Mexico shi ne, koyon ilimi da fasahar zamani na wurin. Wani dalili na daban shi ne, saboda akwai wadatattun albarkatun irrai a nan, ina so in shigo da wasu irrai masu inganci kasar Sin, don kyautata irran mu.”

Ren Jiaojiao, masaniyar kasar Sin da ke aikin binciken masara a "garin" masara_fororder_rjj3

Tun bayan barkewar cutar numfashi ta COVID-19 a shekarar da ta gabata, yanayin annobar da kasar Mexico ke ciki ba kyau. Wannan kuma ya kawo matsaloli da yawa ga aikin nazari na Ren Jiaojiao, har ma ta gaza aiwatar da ayyuka da yawa bisa shirin da aka yi. Amma duk da haka, ba ta yi watsi da kokarinta ba, ta dauki matakin canza aikinta zuwa nazarin manufofi da rubuta kundi. A yayin da ake yakar annobar, Ren Jiaojiao ta shawo kan matsaloli da yawa kuma ta kammala kundin SCI, wanda yanzu aka saka shi cikin wata sananniya mujallar da ta shahara a fannin ilmin shuke-shuke a duniya. Game da nasarar da ta samu kan aikinta a yayin tinkarar annobar, Ren Jiaojiao ta bayyana cewa,

“Nasarar ta ba ni kwarin gwiwa sosai, wadda ta bayyana min cewa, zan iya tsayawa kan kara yin wasu ayyuka. Wannan aikin musaya tsakanin kasa da kasa da aka yi domin masu samun digiri na uku, ya ba ni wata dama mai kyau wajen koyo da mu’amala a wata babbar hukumar kasa da kasa a fannin renon irran masara ta hanyar gadon dabi’un halittu, musamman, na ga wata damar yin musaya mai zurfi a fannin aikin gona a tsakanin kasashen Sin da Mexico. A lokaci guda, ta hanyar irin aikin musaya, na kara fahimtar al'adun kasar Mexico, wanda ya aza harsashi mai kyau ga gudanar da hadin gwiwa da musaya mai zurfi a nan gaba.”