Sharhi: Mu gani a kasa, an ce da kare ana biki a gidan su
2021-08-13 10:36:45 CRI
“Daga ranar 24 ga watan Janairu zuwa ranar 8 ga watan Maris na shekarar 2020, an tura kungiyoyin ma’aikatan lafiya 346, da likitoci dubu 42.6, da ma sauran ma’aikatan kula da lafiyar al’umma sama da 900 zuwa lardin Hubei. Sa’an nan, an shafe sama da kwanaki 10 ne kacal wajen gina asibitin Huoshenshan, da na Leishenshan, da ma wasu asibitocin wucin gadi 16. Gaba daya an warkar da wadanda suka harbu da cutar Covid-19 3000 da shekarunsu ya zarce 80, da ma wasu 7 da shekarunsu ya wuce 100, matakin da ya bayyana yadda kasar Sin take martaba rayukan al’ummarta.”
A jiya ne ofishin watsa bayanai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya fitar da takardar bayani, mai taken“Matsakaiciyar wadata daga dukkanin fannoni: kari kan nasarori da Sin ta cimma a fannin kare hakkokin bil adama”,wadda ta yi nuni da cewa, yadda kasar Sin ta mai da jama’a da rayukansu a gaban komai, duk da munanan hasarorin da ta biya, ya sa ta sauya yanayin annobar da ta samu kanta a ciki, har ma ta kai ga kiyaye tsaron rayukan jama’arta da ma lafiyarsu.
Annobar Covid-19 kalubale ne mafi muni da dan Adam ke fuskanta ta fannin kiwon lafiya cikin shekaru sama da 100 da suka wuce, wadda kuma ta kasance babbar jarrabawa ga kasa da kasa. Sai dai idan mun kwatanta matakan da kasa da kasa suka dauka, da ma sakamakon da suka samu, za mu iya gano babban bambanci, wanda kuma ya shaida mana hakikanin matsayin da suka dauka game da batun hakkin bil Adam.
Tun bayan bullar cutar a kasar, Sin ta dora matukar muhimmanci a kanta, tare da daukar kwararan matakai, inda ta yi iyakacin kokarin samar da jiyya ga masu harbuwa da cutar, baya ga kuma manufofin da ta dauka ta fannin kudi, na tabbatar da duk wadanda suka kamu da cutar za su iya samun damar samun jiyya, matakan da suka kara adadin wadanda suka warke daga cutar. Ban da haka, ta kuma gaggauta yi wa al’umma rigakafi, don su samu kariya daga cutar. Duk da babban kalubalen da take fuskanta a gida, ta kuma yi kokarin samar da tallafi ga kasa da kasa.
Kawo yanzu, kasar Sin ta riga ta samar da alluran rigakafi sama da miliyan 700 ga kasashen duniya, kuma kasashe masu tasowa da ke Asiya da Afirka da ma Latin Amurka sun karbi sama da kaso 90% na rigakafin.
Idan kuma mun duba Amurka, wadda a cewarta, ita ce abin koyi ta fannin kare hakkin bil Adam. Duk da cewa ta fi sauran kasashe ci gaban harkokin kiwon lafiya a duniya, amma ga abin da ya faru a kasar. Tun farkon bullar cutar, ta zama abin da jam’iyyun siyasa na kasar ke amfani da shi wajen gwagwarmayya da juna. Don neman sake cin zaben shugabancin kasar, tsohon shugaban kasar Donald Trump ya yi watsi da gargadin da masana suka yi, kafin daga bisani annobar ta bazu da sauri a kasar. Daga nan, sai aka rika cusa siyasa cikin matakan da suka shafi kadagarkin cutar, ciki har da gwajin cutar, da sanya marufin baki da hanci, da kiyaye takarar cudanyar mutane da rigakafi da sauransu, lamarin da ya sa Amurka ta rasa damammaki da dama na shawo kan cutar, kuma Amurkawa da dama ma sun rasa rayukansu. Don boye gazawarta kuma, sai ta rika siyasantar da cutar, don dora laifi kan wasu, matakin da kuma ya lalata hadin gwiwar kasa da kasa ta fannin dakile cutar.
Ya zuwa ranar 11 ga wata, yawan masu kamuwa da cutar a Amurka, ya wuce miliyan 36 baki daya, yayin da mutane fiye da dubu 610 suka rasa rayukansu, alkaluman da suka zama na farko a duniya, wadanda suka shaida matsayin da kasar ke dauka game da hakkin bil Adam, wato harkokin siyasa sun fi rayukan jama’a. Lallai, kamar yadda bahaushe kan ce, “Mu gani a kasa, an ce da kare ana biki a gidan su”Wato idan har Amurka na fatan zama kan gaba wajen kare hakkokin bil adama, to kamata yayi a ga hakan a zahiri ta hanyar baiwa rayukan al’ummun ta kariya bisa adalci. Ko shakka babu, rayuwa ita ce mafi muhimmanci a dukkanin hakkokin dan Adam. Surutu kan hakkin dan Adam ba shi da wani amfani idan babu rai.
Aikin kare hakkin bil Adam abu ne da za a iya dada kyautata shi. Kasar Sin ta dade da samun gaggaruman nasarori ta fannin kare hakkin dan Adam, bisa tushen martaba hakkokin dan Adam na rayuwa da na ci gaba, inda ta cimma burin saukaka fatara, shekaru 10 kafin cikar wa’adin muradun MDD na samun dauwamammen ci gaba nan da shekarar 2030, kuma matsakacin tsawon rayuwar ‘yan kasar ma ya wuce shekaru 77. Duk da haka, kasar tana kuma fuskantar kalubale sakamakon yawan al’ummarta, da rashin daidaiton ci gaban sassa daban daban. Amma bisa ga manufar mai da jama’a a gaban komai, akwai imanin cewa, kasar Sin za ta samu karin nasarori ta fannin kare hakkin bil Adam. (Lubabatu)