logo

HAUSA

Amurka Kasa Ce Mai Son Dora Laifi Kan Wasu

2021-08-13 15:32:53 CRI

Amurka Kasa Ce Mai Son Dora Laifi Kan Wasu_fororder_微信图片_20210813153236

BY CRI HAUSA

Shahararren masanin Amurka Graham Allison ya ce, tun bayan barkewar cutar COVID-19, ‘yan siyasar Washington sun rika dora laifinsu kan kasar Sin saboda gazawarsu na daukar matakan tinkarar cutar wadda ta kara tsanani a kasar.

Gwamnatin Amurka ta yi biris da gargadin da Sin da WHO suka yi mata a farkon bullar cutar, lokaci mafi muhimmanci wajen dakile ta. Don dora laifi kan kasar Sin, Shugaban kasar a waccan lokaci ya kira wannan cuta da “Kwayar cutar kasar Sin” ko “Kwayar cutar Wuhan” yayin da cutar ke yaduwa a kasar.

An gudanar da babban zaben kasar Amurka a bara, inda ‘yan siyasa suka yi amfani da wannan batu don neman samun goyon baya daga masu kada kuri’u. Bayan kammala zaben, mambobin jam’iyyar Demokuradiyya masu mulkin kasar sun ba da umarni ga hukumar leken asiri da ta gabatar da rahoton binciken asalin cutar cikin kwanaki 90, daga baya kuma sun tilasta WHO ta yi binciken gano asalin cutar a zagaye na biyu a kasar Sin.

Shafin yanar gizo na kwamiti mai kula da harkokin kasa da kasa na Rasha ya ba da wani bayani inda ya ce, matsalar cutar na kara tsananta a Amurka, kuma gwamnati mai ci ba ta mai da hankali kan daidaita zaman oda da doka a kasar ba, a maimakon haka tana yunkurin dora laifi da shafa bakin fenti kan wasu, wanda abu ne da bai dace ba. Ban da wannan kuma, masanin Birtaniya Martin Jacques ya bayyana a wata muhawara cewa, siyasa ta maye gurbin kimiyya tun bayan barkewar wannan cutar.

To, yaushe ne hakikanin lokacin barkewar cutar a Amurka? Ta wacce hanya kwayar cutar ta yadu? Shin ko akwai alaka tsakanin dakin gwajin kwayoyin hallitu na Fort Detrick da kwayar COVID-19? Game da wadannan shakku da ake yi, jama’ar kasashe da dama sun sa hannu a kan Intanet don neman WHO da ta yi bincike.

Bai kamata Amurka ta dora laifi kan wasu ba, kamata ya yi ta sauke nauyin dake wuyanta ta dakatar da yunkurinta. (Amina Xu)