Gasar Olympic ta birnin Tokyo ta kammala a gabar da duniya ke fuskantar yaduwar annobar COVID-19
2021-08-12 16:33:30 CRI
Gasar Olympic ta birnin Tokyon kasar Japan, ta kammala cikin nasara a gabar da duniya ke fuskantar yaduwar annobar COVID-19. Kafin hakan, an bude gasar da kade kade da wake wake, da shagulgulan da suka karade sassan filayen gasar ta Olympic a Tokyo.
An gudanar da kasaitacciyar gasa ciki kwanaki 16, a ajujuwan gasar, wadda taken ta a bana ya zamo “goyon bayan juna, a gabar da ake yaki da cutar COVID-19”.
Wasu ‘yan wasa na cike da murmushi, wasu kuka, wasu sun yi gumi, wasu kuma sun zubar da jini sakamakon rauni, yayin da suke fafatawa a ajin gasanni da aka gudanar cikin nuna kwarewa. Masharhanta na cewa, za a jima ana tuna hadin gwiwa da sassan ‘yan wasa da mashirya gasar suka nunawa juna, yayin fama da COVID-19 da ta haifar da tarnaki ga gasar.
A kalaman shugaban kwamitin shirya gasar ta Olympic Thomas Bach, lokacin bikin rufe gasar ta birnin Tokyo ta 2020 da aka kammala a karshen makon jiya, gasar na cike da kyakkyawan fata, da hadin kai da kwanciyar hankali.
Bach ya ce "An gudanar da gasar Olympic mai kayatarwa. Mu a kwamitin IOC, da abokan aiki na Japan da kawayen mu, mun yi aiki tukuru domin tabbatar da nasarar wannan gasa. Aiki ne na hadin gwiwar mu baki daya.
Sauri, nisa da karfi
‘Yan wasan motsa jiki sun yi gumi yayin da suke shirin tunkarar wannan gasa, duk da dage ta da aka yi da shekara guda saboda annobar COVID-19. Da shigar su cikin gasar kuwa, sai suka sanya himma da kwazo don cimma nasarar lashe lambobin yabo kamar yadda aka saba a duk gasar Olympic.
Kasashe da yankuna 65 sun lashe lambobin zinari 339 a yayin gasar, kana tawagogi 93 sun samu lambobin karramawa. Kasashen Philippines, da Qatar da Bermuda, sun lashe lambobin zinari a karon farko a gasar ta bana a tarihin su.
A jerin kasashe dake sahun gaba wajen lashe lambobin yabo kuwa, Amurka ce ta farko da lambobin zinari 39, da azurfa 41, da tagulla 33. Sai kuma Sin da ta shiga gasar da ‘yan wasa 431, inda ta lashe zinari 38, da azurfa 32 da kuma tagulla 12, daidai da wadanda ta lashe a gasar Olympics ta binrin London a shekarar 2012, da karramawar ‘yan wasa mafi nuna hazaka a wasannin kasashen ketare.
Tawagar ‘yan wasan Sin a wannan karo ma, ita ta mamaye fannin wasan daga nauyi, da ninkaya da kwallon tebur, inda ta rasa lambar karramawa daya tilo a wadannan wasanni. Sai kuma gasar harbi, da badminton da wasannin juya jiki na alkahura, inda a wasanni nau’oi 6 ta hada lambobin zinari 28.
Cikin ‘yan wasa mafiya nuna bajimta, dan wasan Sin Ma Long mai shekaru 32 da haihuwa, wanda kuma shi ne kyaftin din tawagar kasar a wasan tennis, ya zamo mafi samun lambobin yabo a daukacin gasannin Olympics da aka gudanar a tarihi, inda a yanzu yake da lambobin zinari 5.
Sai kuma Lyu Xiaojun, ‘yar wasan daga nauyi ajin masu nauyin kilogiram 81, ‘yar wasan ta Sin mai shekaru 37, ta karya matsayin bajimta na kasancewa mafi yawan shekaru a gasar Olympics da ta halarci gasar a bana.
Akwai kuma ‘yan wasa masu karancin shekaru ko ‘yan "Generation Z", wadanda a bana suka nuna hazaka kwarai, ‘yar wasan kasar Sin Quan Hongchan mai shekaru 14, ta zamo mafi karancin shekaru da ta nuna bajimta cikin tawagar kasar Sin, inda ta lashe maki 3 cikakku, cikin jimillar maki 5 na gasar linkaya, ta kuma yi nasara a gasar ajin mata ta linkayar mita 10.
Sai dai kuma gasar Olympics ta wuce batun lashe lambobin yabo ko karya matsayin bajimta kadai, domin kuwa gasar na kasancewa wata dama ta baiwa ‘yan wasa zarafin cika burin su.
‘yan wasan juya jiki da alkahura Oksana Chusovitina mai shekaru 46 da haihuwa daga kasar Uzbekistan, bata cimma nasarar lashe lambar zinariya ba, a gasar Olympic karo na 8 da ta halarta a bana, amm duk da haka, ta samu yabo da karramawa daga alkalai, da masu aikin sa kai, da ‘yan jarida da sauran ma’aikatan gasar, inda suka mike tsaye tare da yi mata tafi, domin karrama tarihin da ta kafa a gasar.
A daya bangaren kuma, Hend Zaza mai shekaru 12 da kwanaki 204 a duniya daga kasar Syria mai fama da yaki, ta zamo mafi kankantar shekaru da ta halarci gasar ta birnin Tokyo a bana. Bayan kammala gasar kwallon tebur da ta shiga, Zaza ta ce makasudin ta shi ne yin gwagwarmaya domin cimma buri, da aiki tukuru wajen haye wahalhalu, har sai ta kai ga cimma nasarorin da ta sanya gaba.
Tafiya tare da juna
A cewar Mr. Bach, a wannan gaba da ake fama da kalubalen annobar COVID-19, lokaci ne da ya dace duniya ta yi hadin gwiwa da juna a sassa daban daban. Cikin kwanaki sama da 16, ‘yan wasa sun burge mu da nasarori da suka cimma, mun yi farin ciki, wasu sun yi hawaye, kun kafa tarihin gasar Olympic mai kayatarwa. Ya ce "Kun yi sauri cike da kuzari, kun daga sama, kun nuna karfi, saboda dukkanin mu mun kasance tare cikin hadin gwiwa.
Kafin bude gasar Olympics ta birnin Tokyo, kwamitin IOC ya amince da sanya kalmar "together" wato tare, cikin jerin kalmomin da a baya ake dangantawa da gasar Olympic, wato "Sauri, nisa, karfi". An cimma wannan matsaya ne a yayin taron IOC na 138, wanda shi ne karon farko da aka yi irin wannan sauyi a taken gasar cikin sama da shekaru 120.
Bach ya kara da cewa, “Hadin kai shi ne ke ingiza cimma nasarar duniya, har ta zama wuri da kowa ke jin dadin sa ta hanyar wasanni. Ya ce “Za mu iya kara sauri, mu kara nisa, amma za mu kara karfi ne kawai idan mun yi aiki tare da juna cikin hadin gwiwa. Muna son kara maida hankali ga goyawa juna baya. Shi ne ma’anar kalmar 'tare', wato goyawa juna baya".
Mr. Bach ya ce “A yayin gasar birnin Tokyo, mun ga yanayi masu taba zuciya daga ‘yan wasa na sassan duniya daban daban, da suka rika nunawa juna karamci. An rika musayar rigunan wasa, da taya juna murna, ko musayar kalaman karfafa gwiwar juna, an sanyawa gasar wani karsashi mai kima, duk da an gudanar da ita ba tare da ‘yan kallo ba a mafi yawan filayen ta”.
A hukumance, an aiwatar da matakai na dakile yaduwar annoba, ciki har da gwaje gwaje, da feshin maganin kashe kwayoyin cuta, da ba da tazara a duk inda ya wajaba domin tabbatar da gudanar gasar cikin tsaron lafiya. Kaza lika a cewar Bach, an gudanar da gwajin COVID-19 42,500 a farko na isar ‘yan wasa, inda kason da aka samu na masu dauke da ita bai wuce kaso 0.08 % a ranar 5 ga watan Agusta ba. Sai kuma karin gwaji 571,000 daga baya, wanda ya samar da sakamo kaso 0.02% na masu dauke da cutar.
Babban jami’in na kwamitin IOC ya kara da cewa, "Ina ganin a iya cewa daukacin masu tallafawa gudanar da gasar a nan birnin Tokyo cikin ‘yan makwanni kalilan, sun shirya sosai a fannin gudanar da gwajin cutar sama da wurare da dama a duniya".
Sai kuma mun hadu a Paris
Nan da shekaru 3 masu zuwa ne za a sake haduwa, a gasar Olympic ta lokacin zafi da birnin Paris zai karbi bakunci, lokacin da zai yi daidai da cika shekaru 100, tun bayan da birnin ya karbi bakuncin gasar a karon karshe.
Yayin bikin rufe gasar Tokyo a Lahadin karshen mako, gwamnan birnin Yuriko Koike, ya mika tutar Olympic ga Mr. Bach, wanda shi kuma ya mika ta ga magajin garin birnin Paris Anne Hidalgo.
Kuma a karon farko a tarihi, a yayin bikin rufe gasar Olympics, aka gudanar da bikin karbar bakuncin gasar daga birnin da zai karbe ta a karo na gaba, wato a shekarar 2024. An gano shugaban Faransa Emmanuel Macron, na gabatar da taken gasar ta gaba, wato "Sauri, nisa, karfi da kuma yin aiki tare".
Kaza lika yayin wani taron manema labarai da ya gudana, an jiyo shugaban kwamitin shirya gasar Olympic ta birnin Paris Tony Estanguet na cewa, “Ko wacce gasar Olympics na ba da gudummawa ta daban, ta yadda hakan ke kara bunkasa armashin gasar. Burin mu a gasar Paris ta 2024, shi ne mu gabatar da wasanni da za su karbi bakuncin al’umma, sama da na duk wani lokaci a baya.
A cewar Tony Estanguet, gasar Paris na da burin baiwa dubun dubatar al’umma damar shiga kallon ta, da shagulgula da za gudanar masu kayatarwa a bakin kogin Seine.
Yanzu haka dai ana iya cewa, mun yi ban kwana da Tokyo. Kuma birnin Paris na yiwa duniya maraba.