logo

HAUSA

Sin Ta Yi Rawar Gani A Fannin Kare Hakkin Bil Adama

2021-08-12 17:38:09 CRI

Sin Ta Yi Rawar Gani A Fannin Kare Hakkin Bil Adama_fororder_0812-01

A ranar Alhamis din nan ne ofishin watsa bayanai na majalissar gudanarwar kasar Sin ya fitar da sabuwar takardar sanarwa, game da ci gaban kasar a fannin kare hakkin bil adama, karkashin manufar cimma burin samun matsakaiciyar wadata.

Takardar mai lakabin "Matsakaiciyar wadata daga dukkanin fannoni: kari kan nasarori da Sin ta cimma a fannin kare hakkokin bil adama", ta yi bayani dalla dalla, game da manufofin kasar, masu nasaba da samar da matsakaiciyar wadata, wadda ke wakiltar cikakken ci gaban kasar karkashin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, da gwamnati da ma daukacin Sinawa a fannin kare hakkin bil adama a Sin, tare da sabuwar gudummawar ta ga kudurin kare hakkokin bil adama na duniya baki daya.

A duk mai bibiyar irin ci gaba da Sin ke samu a wannan fanni, ya kwana da sabin nasarori da kasar ta cimma a bangarori da dama, musamman a shekarun baya bayan nan, kama daga cimma nasarar yakar matsanancin talauci, da nasarar farfadowar kasar a zamanance, zuwa ga aiwatar da managartan matakan kare hakkin bil adama a gida, da kuma gudummawar hakan a mataki na kasa da kasa.

A zahiri take cewa, mahukunta a kasar Sin sun yi namijin kokari wajen sauya akalar tarihin kasar, ta hanyar kawar da kangin fatara, ta yadda a yanzu haka al’ummun Sinawa ke samun isasshen abinci da tufafi, da muhalli mai inganci, da kuma matsakaiciyar wadata.

Shaidu na zahiri na nuna yadda Sinawa ke rayuwa cikin kyakkyawan yanayin tattalin arziki, bisa salon siyasa mafi dacewa da kasa, da ingancin al’adun gargajiya, da daidaito tsakanin sassan al’ummun kasar.

Sauran sassan sun hada da ingancin tsarin kiwon lafiya, da raya muhallin halittu. A hannu guda kuma, gwamnatin kasar na kara aiwatar da matakai na rage gibin ababen more rayuwa tsakanin birane da yankunan karkara, ta yadda hakan ke amfanar daukacin al’ummunta.

Dukkanin wadannan matakai, ana iya cewa su ne ginshikai na kare hakkokin bil adama na gaskiya, sabanin yadda wasu kasashen yamma ke daukar batun kare hakkin bil adama a matsayin makami na siyasa, suna yada jita jita maras tushe. (Saminu Alhassan)