logo

HAUSA

Kasar Sin tana himmatuwa wajen sauke nauyinta a fannin tinkarar sauyin yanayi

2021-08-12 11:24:04 CRI

Kasar Sin tana himmatuwa wajen sauke nauyinta a fannin tinkarar sauyin yanayi_fororder_A

Idan mun dubi “ajandar diflomasiyya” ta shugaban kasar Sin a farkon rabin shekarar da muke ciki, muna iya gano cewa, akwai batutuwa da dama da suka shafi shawo kan matsalar sauyin yanayi, ciki har da alkawarin da shugaban kasar Sin ya yi a fannin tinkarar sauyin yanayi, a yayin dandalin tattaunawa kan tattalin arziki na Davos, inda ya yi kira da a inganta hadin-gwiwar Sin da Turai wajen tinkarar sauyin yanayi, a shawarwarin shugabannin Sin da Faransa da Jamus, da kuma bullo da shawarar gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya dake kunshe da dan Adam, da halittu, a wajen taron koli kan yanayi tsakanin shugabannin kasa da kasa. Kasar Sin tana iya kokarinta wajen sauke nauyin dake wuyanta, na shawo kan matsalar sauyin yanayi.

“Wannan hanya ce ta sada zumunta, amma mazauna wurin suna kiran ta ‘hanyar kasar Sin’……”

A sabon gari na birnin Vientiane dake kasar Laos, akwai wani yankin raya sana’o’i mai suna Saysettha, wanda kasashen Sin da Laos suka bunkasa shi cikin hadin-gwiwa, kuma ba tare da gurbata muhalli ba. Babban manajan kamfanin zuba jari na hadin-gwiwar Sin da Laos dake kula da ayyukan yankin, Liu Hu ya ce, akwai kayayyaki da na’urori da dama da kasar Sin ta tallafawa yankin, ciki har da fitilun tituna masu amfani da hasken rana, da motoci masu amfani da sabbin makamashi da sauransu, al’amarin da ya taimaka sosai ga ci gaban sabon garin Vientiane, har ya zama tamkar abun misali a fannin kiyaye muhallin halittu a kasar Laos da ma duk yankin kudu maso gabashin nahiyar Asiya.

Sakamakon yaduwar cutar COVID-19, ana ta kara zurfafa tunani game da dangantakar dake tsakanin dan Adam da halittu. Daidaita yanayin duniya yana fuskantar wasu manyan kalubaloli da ba’a taba ganin irinsu ba a tarihi, ciki har da yawan samun yanayi mai tsanani, da bacewar kasantuwar halittu daban-daban, da tsanantar kwararar hamada.

A ranar 22 ga watan Afrilun bana, wato “ranar duniyarmu” karo na 52, shugabannin kasashe da na kungiyoyin kasa da kasa su 40, sun hallara don halartar taron koli kan batutuwan yanayi ta kafar Intanet, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bullo da shirin kasarsa na “gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya, dake kunshe da dan Adam da halittu”, inda ya ce,

“Sauyin yanayi na haifar da babban kalubale ga rayuwa gami da ci gaban dan Adam, ya dace kasa da kasa su gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya dake kunshe da dan Adam da halittu tare. Ya kamata dan Adam ya mutunta muhallin halittu da kiyaye shi.”

Kasar Sin tana himmatuwa wajen sauke nauyinta a fannin tinkarar sauyin yanayi_fororder_B

A nasa bangaren kuma, babban magatakardan Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya ce, 2021 shekara ce mai matukar muhimmanci ga kasa da kasa wajen tinkarar sauyin yanayi. A shekaru biyar da suka gabata, sama da kasashe 70 sun rattaba hannu kan yarjejeniyar Paris, wadda ta kasance muhimmiyar yarjejeniyar duniya a fannin shawo kan sauyin yanayi. Bana ta zama shekarar da ake aiwatar da yarjejeniyar daga dukkan fannoni, kuma za’a gudanar da babban taro kan sauyin yanayi na MDD karo na 26 a kasar Birtaniya, inda ake sa ran taron zai zama muhimmin mafari ga daukar matakai na bai daya.

Kyan alkawari cikawa. A watan Satumbar bara, yayin da yake halartar babban taron MDD karo na 75, shugaba Xi ya sanar da burika biyu da kasar Sin take kokarin cimmawa, wato yawan hayaki mai dumama yanayin duniyarmu da za ta fitar, zai kai matsayin koli kafin shekarar 2030, sannan za ta yi kokarin samun daidaito tsakanin yawan hayakin da za ta fitar, da yawan abubuwan da za su shawo kan hayakin kafin shekarar 2060.

Shugaba Xi ya jaddada cewa, wannan shi ne matakin da kasar Sin ta dauka bisa radin kanta, amma ba don matsin lamba daga saura ba, inda ya ce,

“Muna ganin cewa, duk wani abun da zai haifarwa daukacin al’umma alheri, ya kamata kasar Sin ta yi shi da kyau. A halin yanzu, kasar Sin tana tsara shirinta, da fara daukar wasu matakai, don tabbatar da cimma wadannan burika.”

Kasar Sin ta dade tana bayar da gudummawarta wajen kyautata muhallin halittun duniya. A shekara ta 2020, yawan hayaki mai dumama yanayi da kasar ta fitar ya ragu da kaso 48.4 bisa dari, idan aka kwatanta da na shekara ta 2005. Kana, yawan motoci masu amfani da sabbin makamashi da kasar ta sayar ya dauki kaso 55 bisa dari na duk duniya. A watan Oktobar bana ma, kasar za ta karbi bakuncin babban taro karo na 15 tsakanin kasashen da suka daddale yarjejeniyar kasancewar halittu daban-daban, a wani kokari na kara kiyaye nau’o’in halittu daban-daban a duk fadin duniya.   (Murtala Zhang)