logo

HAUSA

Rawar Da ’Yan Wasan Kasar Sin Suka Taka A Gasar Olympics Ta Birnin Tokyo Ta Kara Nunawa Duniya Yadda Kasar Take Bunkasa Cikin Sauri

2021-08-11 16:33:42 CRI

Rawar Da ’Yan Wasan Kasar Sin Suka Taka A Gasar Olympics Ta Birnin Tokyo Ta Kara Nunawa Duniya Yadda Kasar Take Bunkasa Cikin Sauri_fororder_0811-1

Ranar Lahadi 8 ga watan Agustan shekarar 2021 ne, aka rufe gasar wasannin motsa jiki ta Olympics karo na 32 a birnin Tokyon kasar Japan, gasar da a baya aka shirya gudanarwa, a shekarar 2020, amma aka dage ta saboda annobar COVID-19 dake ci gaba da addabar sassan duniya.

Wannan ne ma ya sa a lokacin bikin bude gasar, kimanin matune 950 ne kawai, ciki har da jami’ai da ’yan jarida aka bari suka shiga wajen bude wasannin mai daukar mutane dubu 68. Gasar wasannin Olympics ta kammala a birnin Tokyo, ta janyo hankalin ’yan wasa 11,000 daga tawagogi 205 da kungiyar wasannin Olympics ta ’yan gudun hijira. Sai dai duk da matakan yaki da annobar COVID-19 da aka dauka a lokacin gasar, hakan bai dakushe ruhi da armashin gasar. Sai dai ba kamar yadda aka saba a baya ba, a wannan karo, duk ’yan wasan da suka kammala rukunin wasanninsu, aka kuma ba su lambobin da suka lashe, sai kowa ya kama hanyar dawo wa gida, sabanin yadda kowa ke tsaya bisa al’ada har zuwa lokacin kammala gasar baki daya.

A wannan karo, kasar Sin ta tura tawaga mai kunshe da mambobi 777 zuwa Tokyo, kuma wannan ita ce tawagar ’yan wasa mafi yawa da ta taba turawa zuwa ketare. ’Yan wasan kasar Sin 431 ciki har da zakarun wasannin Olympics 24 ne, suka fafata a wasanni 30 daga cikin 33 da aka fafata a gasar birnin na Tokyo.

Shugaban kwamitin shirya gasar wasannin Olmypics na kasa da kasa Thomas Bach ya ce, nasarorin da ’yan wasan kasar Sin suka cimma a wasanni daban-daban ta yi matukar birge shi, kuma hakan zai kara nunawa duniya yadda kasar Sin ke bunkasa cikin sauri. Ya kuma yi imanin cewa, gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta birnin Beijing da za a gudanar a watan Faburairun shekarar 2022, za ta kayatar da duniya. Masana na cewa, irin matakan yaki da annobar COVID-19 da aka dauka a lokacin gasar, za su taimaka a gasar Olympics ta Beijing dake tafe.

A ranar 5 ga watan Satumban shekarar 2021 ne, za a gudanar da gasar Olympics ajin nakasassu a birnin na Tokyo. Wannan ita ce gasar Olympics ta 2 da aka gudanar a kasar Japan. Wani abin farin ciki shi ne, duk da matakan yaki da annobar COVID-19 da aka dauka a lokacin gasar, kama daga rashin halartar ’yan kallo kamar yadda aka saba, hakan bai dakushe ruhi da armashin gasar ba. Bukatar Kuku dai wanka. Bayan kammala gasar ce kuma, aka mikawa birnin Paris na kasar Faransa tutar shirya gasar ta gaba, matakin dake alamanta cewa, shi ne zai karbi bakuncin gasar da za a gudanar a shekarar 2024. (Ibrahim Yaya)