logo

HAUSA

Ayyukan Raya Kasa A Zambia Sun Tabbatar Da Kasancewar Kasar Sin Aminiya Ta Hakika

2021-08-10 17:18:10 CRI

Ayyukan Raya Kasa A Zambia Sun Tabbatar Da Kasancewar Kasar Sin Aminiya Ta Hakika_fororder_0810-01

Har kullum, kasar Sin na ci gaba da nuna matsayinta na babbar kasa mai kaunar ci gaban kasashe masu tasowa musamman kasashen Afrika, duk da yanayi na rashin tabbas da kalubalen tattalin arziki da fititinun da kasashen yammacin duniya ke son tadawa. Misali na baya-bayan nan game da wannan batu shi ne, yadda hadin gwiwa tsakanin Sin da kasar Zambia dake kudancin Afrika ke kara haifar da sakamakon a zo a gani. A jiya Litinin, shugaban kasar Edgar Lungu, ya kaddamar da sabon sashen tashi da saukar jiragen sama na biyu a filin jirgin saman kasa da kasa na Kenneth Kaunda dake babban birnin Lusaka na kasar. A yanzu haka, filin jirgin saman kan yi jigilar fasinjoji miliyan 2 ne a kowacce shekara, amma da wannan ci gaba da aka samu, za a samu ninkin wannan adadi. Baya ga zamanantar da kasar da wannan aiki da kamfanin kasar Sin yake aiwatarwa, zai kuma kara biyan bukatun sufuri na al’ummar kasar ga kuma uwa-uba habaka tattalin arzikin bangaren sufurin kasar. Har ila yau, zai kara samar da karin guraben ayyukan yi, bisa la’akari da cewa bayan kammala aikin baki daya, za a samu otel da sashen tashi da saukar kayayyaki da ginin cibiyar kula da sufurin jirage da ofishin kashe gobara da na ceto tare da kantin sayayya.

Ban da wannan, a makon da ya gabata ma, shugaban kasar ya kaddamar da sabon filin jirgin saman kasa da kasa na Simon Mwansa Kapwepwe, wanda shi ma kasar Sin ce ta samar da kudin gina shi ta hannun bakin ta na EXIM na kasar Sin. Kamar yadda shugaban ya bayyana, an ce, wannan wani babban aiki ne da ya cancanci yabo matuka, domin zai taimaka wajen bunkasa harkokin yawon shakatawa da ajandar zamanantar da masana’antun kasar. Haka kuma zai kara samar da kwarin gwiwa da aminci a zukatan al’ummar kasar dangane da gwamnatin, duba da cewa, ya yi daidai da alkawarin gwamnatin kasar na farfado da ababen more rayuwa da zama cibiyar sufuri a yanki. Hakika kasar Sin ta yi namijin kokari domin taimakonta zai ceci kasar da kai ta ga sabon matsayin samun ci gaba, wanda zai kara kawo kwanciyar hankali da wadata. Haka zalika ya kara tabbatar da kasar Sin a matsayin aminiya ta hakika, kuma abun dogaro, komai wuya komai dadi. (Fa’iza Mustapha)