logo

HAUSA

Anthony Fauci: Gasar tseren babura ta Sturgis za ta yada kwayar cutar COVID-19 ta gama gari

2021-08-09 11:10:05 CRI

Anthony Fauci: Gasar tseren babura ta Sturgis za ta yada kwayar cutar COVID-19 ta gama gari_fororder_src=http___n.sinaimg.cn_spider20210805_200_w640h360_20210805_a9f0-fb82efa5f60e15cf46b93a5e6d00aaca.png&refer=http___n.sinaimg

Jiya Lahadi, mai ba da shawara ga fadar White House kan harkokin kiwon lafiya Anthony Fauci, ya bayyana damuwarsa game da gasar tseren babura ta Sturgis, wadda za a gudanar a jihar South Dakota. Yana mai zargin jagoran gasar da mahalartan ta da cewa, za su yada kwayar cutar COVID-19 gama gari.

A cewarsa, masana kimiyya a cibiyar nazarin tattalin arzikin kiwon lafiya da manufofi na jami’ar San Diego, sun fidda sakamako bayan cikakken nazarin da suka yi, inda suka ce gasar da aka gudana a bara, ta haddasa harbuwar mutane kimanin dubu 266 da cutar, kuma idan an ci gaba da gudanar da ita a bana, adadi zai karu zuwa miliyan 700.

To sai dai kuma jim kadan da tsokacin na Fauci, gwamnar jihar South Dakota Kristi Noem, ta ba da sanarwar gaggawa, tana musanta ra’ayin masanin. A cewar ta, Mr. Fauci na keta hakkin jama’a, kuma yana fakewa da batun kimiyya ne don sukar masu shiga gasar. (Amina Xu)