logo

HAUSA

Amurka ta sake tsoma baki cikin harkokin yankin Hongkong na kasar Sin

2021-08-06 15:32:39 CRI

Amurka ta sake tsoma baki cikin harkokin yankin Hongkong na kasar Sin_fororder_微信图片_20210806153223

Sakataren harkokin wajen kasar Amurka Antony Blinken ya ba da bayani a kan shafin sada zumunta a jiya cewa, bisa umurnin shugaban kasar na tsawaita lokacin tilasta barin kasar, Amurkar za ta baiwa wasu mutane mafaka dake tsoron komawa yankin Hongkong.

Yankin Hongkong ya koma hanyar samun bunkasuwa mai wadata bayan aiwatar da dokar tsaron kasa a yankin, amma wasu ’yan siyasar Amurka suna ci gaba da goyon bayan ’yan aware, don kawo barazana ga yankin da nufin kawo cikas ga bunkasuwar kasar.

A matsayin kasar dake kan gaba a fannin yawan masu harbuwa da cutar COVID-19 da yawan mamata sakamakon cutar, a sa’i daya kuma, yawan masu aikata laifufuka sun karu matuka a wurare daban-daban na kasar Amurka, har jihar New York ta sanar da shiga halin ko ta kwana. A hakika dai, halin da Amurka ke ciki yanzu ba zai dace da bada mafaka ga wadannan ’yan aware ba.

Yanzu, hankulan fararen hula na yankin Hongkong a kwance suke, kuma mazauna sun fahimci cewa, dokar tana ba da tabbaci ga jama’ar da bakin dake yankin a fannin hakkoki da ’yancin kai.

Don haka, Amurka ba za ta cimma nasarar kawo cikas ga yankin ko kasar Sin ba. A maimakon haka, zai fi kyau ta warware matsalolin da ita kanta take fuskanta a fannin tinkarar cutar da matsalolin al’umma, ta baiwa jama’arta mafaka. (Amina Xu)